Hukuncin Aske kan Jariri

Domin neman ƙarin bayani danna nan

Tambaya: Menene Hukuncin Aske kan Jariri?

Amsa: Aske kan jariri Sunnah ne idan jaririn na miji ne, amma akwai tsaɓani game da mace.

An rawaito daga Annabi tsira Da Amincin Allah su tabbata a gare shi yace:

Kowani yaro da aka haifa yana ɗaure da Abin yankan sa, wanda za’a yanka masa ranar bakwai. Sannan za’ayi masa aski, a sanya masa suna.

Tirmidhi: 1522. Abu dawud: 3838

An tambayi masu Fatawa ta Lajnatud-da’imah ta Suudiyya game da Aske kan jaririya mace sai suka ce:

Ba’a shar’anta aske kan jaririya ba

10/468

Malaman Fiqhu sun samu tsaɓani game da aske kan jaririya mace. Malikiyya da Shafi’iyya sun tafi akan cewa za’a aske, kamar yadda ake aske na namiji, amma hanabila sun tafi kan cewa baza’a aske kan mace ba.

Shafi’iyya sunyi Hujja da Hadisi mursal wanda aka rawaito daga Muhammad bin Ali bin Hussain.

Sai faɗima Allah ya ƙara mata yarda ta gwada nauyin Gashin Hassan da Hussain da Zainab da Ummu Kulsum sai ta bada sadaƙar Azurfa kwatankwacin nauyin gashin.

Su kuma Hanabila sun kafa Hujja kan cewa ba Sunnah bane aske kan jaririya mace da cewa Asali shine haramcin aske kan mace idan ba da wata lalura ba, haka nan umarni da yazo kan aske kan jariri yazo ne kan jinjiri na miji.

Allah shine mafi sani.

Leave a Reply

Latest updates
Categories