ASKE GEMU, KO SAISAYE SHI HAR YA KOMA TAMKAR BABU SHI HARAMUN NE(Dr. Ibrahim Jalo Jalingo)

Lalle abin bakin ciki ne matuka
ganin yadda wasu Musulmi suka
maida aske gashin gemunsu wata
hanyar ado ta musamman, wannan
abin bakin ciki ne, saboda Annabi
mai tsira da amincin Allah ya yi
umurni ne da a bar gashin gemu a
kuma yawaita shi.
Imamul Bukhari ya ruwaito hadithi
na 5,892, da Imamu Muslim hadithi
na 259, daga Sahabi Abdullahi
Dan Umar ya ce Annbi mai tsira da
amincin Allah ya ce:-
(( ﺧﺎﻟﻔﻮﺍ ﺍﻟﻤﺸﺮﻛﻴﻦ ﻭﻓﺮﻭﺍ ﺍﻟﻠﺤﻰ ﻭﺍﺣﻔﻮﺍ
ﺍﻟﺸﻮﺍﺭﺏ)).
Ma’ana: ((Ku saba wa Mush’rukai,
ku samar da (gashin) gemma, ku
saisaye gashin baki)). Intaha.
Lalle wajibi ne a kan dukkan
Musulmi maza su tsaida gemu,
haramun ne a kansu su aske
gashin gemunsu, ko su rika
saisaye shi har ya koma tamkar
babu shi.
Wannan lamari wajibi ne a kan
dukkan shugabannimu na
Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah
Wa Iqamatis Sunnah, kuma wajibi
ne a kan dukkan membobinmu na
Kungiyar: ‘Yan agajinmu, da
wadanda suke ba ‘Yan agaji ba.
Allah Ya taimake mu ya nuna
mana gaskiya gaskiya ce Ya ba
mu ikon binta, Ya nuna mana
karya karya ce Ya ba mu ikon guje
mata. Ameen.

2 responses to “ASKE GEMU, KO SAISAYE SHI HAR YA KOMA TAMKAR BABU SHI HARAMUN NE(Dr. Ibrahim Jalo Jalingo)”
  1. mubaraksalaf Avatar

    jazakallahu

  2. jitendra thkariha Avatar
    jitendra thkariha

    entresting

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: