ZAGIN SAHABBAI HARAMUN NE:

Danna nan domin shiga group na karatu Online

By: Dr. Ibrahim Jalo Jalingo



1. Yana daga cikin manyan alamu na bacewar manyan kungiyoyin ‘Yan bidi’ah; Khawaarijawansu, da Shi’awansu, da Naasibawansu: zagin sahabban Manzon Allah mai tsira da amincin Allah.
2. Lalle zagin babban Sahabi Aliyyu Bin Abi Dalib Allah Ya kara masa yarda, da zagin sauran sahabban Annabi mai tsira da aminci Allah manyansu da kananansu laifi ne babba, a gaskiya ma ba ma wai zagin Sahabbai ba Aliyyu, ko Abubakar, ko Umar, ko Uthman ko wasunsu ba ne laifi kawai, a’a zagin ko wane Musulmi ma laifi ne babba a bisa nassin Manzon Allah mai tsira da amincin Allah; Imamul Bukhariy ya ruwaito Hadithi na 48, da Muslim Hadithi na 64, da Tirmiziy Hadithi na 1983, da Nasaa’iy Hadithi na 4108, da Ibnu Majah Hadithi na 69, da Ahmad Hadithi na 3647, da Ibnu Hibban Hadithi na 5939, da Bazzar Hadithi na 1172, da Dabaraaniy Hadithi na 9958 daga Sahabi Abdullahi Bin Mas’ud Allah Ya kara masa yarda cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce:-

((سباب المسلم فسوق وقتاله كفر)).
Ma’ana: ((Zagin Musulmi fasikanci ne yakar shi kuma kafirci ne)).
Ku ‘yan bidi’ah Shi’awanku, da Khawarijawanku, da Nasibawanku ku ne kuke zagin Sahabbai har yau har gobe, ku ne kuma a cikin aqidarku da za ce: Sahabban nan za su dawo duniya a yanzu to kuwa da za ku yake su saboda wannan shi ne ginshikin addininku.
3. Amma su Ahlus Sunnah babu Sahabin da suke zagi ballantana ma su yake shi da za a kaddara cewa zai sake dawowa duniya a yanzu. Sannan su Ahlus Sunnah dukkan abin da ya faru da su Sahabban a zaminsu na zage-zagen juna, ko na yake yaken juna, suna bin abin da Allah Madaukakin Sarki Ya hukunta ne game da yin ta’amuli da hakan; watau na cewa wannan abin da ya faru a tsakaninsu bai fidda su daga Musulunci ba bai kuma fidda su daga Imani ba, a’a suna nan Musulmi Muminai; kamar dai yadda Shi Allah Madaukakin Sarki Ya ce ne cikin Suratul Hujurat aya ta 9-10:-
((وان طائفتان من المؤمنين اقتتلوا فأصلحوا بينهما فان بغت احداهما على الاخرى فقاتلوا التي تبغي حتى تفيء الى امر الله فان فاءت فأصلحوا بينهما بالعدل وأقسطوا ان الله يحب المقسطين. إنما المؤمنون اخوة فأصلحوا بين أخويكم واتقوا الله لعلكم ترحمون)).
Ma’ana: ((Idan aka samu wasu kungiyoyi biyu daga Muminai suka yaki juna to ku yi sulhu a tsakaninsu idan dayar ta yi zalunci a kan dayar to ku yaki wacce take zaluncin har sai ta dawo zuwa ga umurnin Allah, idan ta dawo sai ku yi sulhu a tsakaninsu cikin adalci, ku yi adalci lalle Allah Yana son masu adalci. Abin sani shi ne Muminai ‘yan’uwan juna ne, saboda haka ku yi sulhu a tsakanin ‘yan’uwanku, ku ji tsoron Allah kila a muku rahama)).
Ga shi dai a nan kuna gani karara cikin wadannan ayoyi biyun inda Allah Madaukakin Sarki Ya kira bangarori biyun da cewa su ‘yan’uwan juna ne, Ya kuma siffanta su da cewa su Muminai ne; duk kuwa da cewa suna yakar junansu, suna kashe junansu suna ta zagin junansu. Haka Allah Ya ga dama Ya tabbatar da wannan hukuncin game da Sahabban Annabi mai tsira da amincin Allah; su kuma Ahlus Sunnah sun yarda da dukkan abin da Allah Madaukakin Sarki Ya ce a cikin Alkur’ani mai girma; saboda haka ba sa kore wa Sahabban Musulunci da Imani.
4. Haka nan su Ahlus Sunnah ba sa zagin kowa daga cikin wadannan Sahabban saboda Annabi mai tsira da amincin Allah ya haramta zagin su; Bukhariy ya ruwaito Hadithi na 3673, da Muslim Hadithi na 2540, da Abu Dawud Hadithi na 4660, da Tirmiziy Hadithi na 3861, da Nasaa’iy Hadithi na 8250, da Ibnu Majah Hadithi na 161, da Ahmad Hadithi na 11094, da Ibnu Hibban Hadithi na 7353, da Dabraaniy cikin Kabeer Hadithi na 303 daga Sahabi Abu Sa’id Al-Khudriy, da Sahabi Abu Hurairah Allah Ya Kara musu yarda cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce:-
((لا تسبوا أصحابي فَلَو ان احدكم أنفق مثل احد ذهبا ما بلغ مد احدهم ولا نصيفه)).
Ma’ana: ((Kada ku zagi sahabbaina lalle da dayanku zai ba da sadakar zinarin da ya kai dutsen Uhudu nauyi to da ladan da zai samu ba zai kai ladan da dayansu zai samu ba idan ya yi sadakar mudu guda ko ma rabin mudun da zai ciyar)). Haka nan Dabraaniy ya ruwaito cikin Kabeer Hadithi na 12,541, da Bazzar cikin Musnad Hadithi na 5753 daga Sahabi Ibnu Abbas da Sahabi Ibnu Umar Allah Ya kara musu yarda cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce:-
((من سب أصحابي فعليه لعنة الله والملائكة والنَّاس اجمعين)).
Ma’ana: ((Duk wanda ya zagi Sahabbaina tsinuwar Allah da Mala’iku da Mutane gaba daya ta tabbata a kan shi)).
5. Tabbas Ahlus Sunnah suna gode wa Allah Madaukakin Sarki da ya hore musu mika wuya ga dukkan abin da Allah da MsnzonSa suka ce musu, ko suka umurce su da yi ko da bi. Allah Ya taimake mu. Ameen.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories