AHLUSSUNNAH BASUYIN SASSAUCI GA DUK MAI TSABAWA ALLAH DA MANZONSA

·

·

‘Yan’uwana Musulmai ku dinga yimin uzuri… Wasu suna tsine min, wasu sunace wai ni shaidan ne mai raba kan al’ummah… Ina sake jaddada muku mu musulmai bamu da aqeedar ummah… Ma’ana abar kowa yayi addini bisa fahimtarsa… A’a dolene ayi koyi da annabi(saw) domin shi aka turo mana, babu yadda za’ayi ka gina bautarka bisa fahimtarka ko bisa fahimtar malaminka kawai batare da dace wa da ta annabi ba kayi tunanin kana kan daidai… Dolene mu dinga fadin abinda muka san shine daidai domin da hakane za’a fahimci addini.. Amma da zarar akayi shiru wani har ya mutu bazaisan abinda yakeyi ba… Kuma aduk lokacin da kukaga mu ahlussunnah muna yi wa wasu mabiya wata tafarki raddi, toh ba munayine kawai don mu more ba, A’a munayine domin masu fahimta su fahimta. Bamu kiyayya ga kowa. Bamu fada da kowa. Amma inka tsabawa Allah da manzonsa dole mu fada maka gaskiya. Wannan itace aqeedarmu bamu yiwa mutum kara inhar ya tsabawa Allah da manzonsa….
Yana daga cikin abinda ya dada jefa mabiya tafarkin sufanci ramin bata, bin aqeedar ummah,, alokacin da sukayi wa ‘yan shi’ah kara, sukaki su fita suyi bara’a da da’awar shi’ah, kuma sukaki suyi wa mabiyansu gamsasshen bayani kan aqeedar shi’ah duk da cewa sun san ‘yan shi’ah batattu ne. Kuma suna kan gurbatacciyar aqeedah ne. Da haka shi’ah ta samu gindin zama acikinsu ta cigaba da yaduwa tsakanin matasan sufaye…
Mabiya sufaye a aqeedance munfi kusa dasu fiye da ‘yan shi’ah.. Domin mabiyin tafarkin sufanci ya yarda da qur’ani cikakke ya yarda da hadisi, sannan ya yarda da sahabbai baki daya, ya yarda da matan annabi baki daya. Toh amman ‘yan shi’ah basu yadda da wa’innan ba duka…
Toh amma meyasa ‘yan dariku suke hadin kai da ‘yan shi’ah duk da ‘yan shi’ah suna zagin sahabbai kuma suna zagin matan annabi? Harma da iyayen annabi duk ‘yan shi’ah suna zagi..
Toh gaskiyan lamari shine ‘yan dariku suna hade dasune kawai sabida su ‘yan shi’ah basu zagin waliyyan ‘yan darika irinsu inyass da tidjani….. Wannan shine hakikanin lamari.
Ga kadan daga aqeedojin shi’ah wadda ta tsabawa tafarkin sufanci…
1.Shi’ah sunce iyayen annabi suna wuta.
2.Shi’ah sunce abubakar,umar,usman, da sauran wasu sahabbai(ra) duk kafirai ne.
3.Shi’ah sunce nana Aisha mazinaciyace..
Mabiya tafarkin sufanci ku sake tunani sannan ku koma cikin littafin ashafa kuji me akace game da mai zagin sahabbai…
Mukam bamuyin kara wa kowa. Ko ahlussunnah ne ya kauce dolene mu fada masa, ya dawo ya gyara. Wannan itace ka’idarmu… Kuyi hakuri in kunga muna tsanantawa…. Allah yasa mudace

4 responses to “AHLUSSUNNAH BASUYIN SASSAUCI GA DUK MAI TSABAWA ALLAH DA MANZONSA”
 1. A.A Maradun Avatar
  A.A Maradun

  Allah gafarta Malam Allah ya saka da alheri, a dan rinka lura da kaidojin rubutun hausa gwargwadon hali, misali: “saba wa” ya kamata a ce ba “tsabawa” ba;haka kuma a kula da hade kalmomin da ba a hadewa misali a rubuta “mazinaciya ce” ba “mazinaciyace ba” haka kuma “ba mu yin” ya kamata ba “bamuyin” ba. Da dai sauran su. Allah sa mu gane kuma mu gyara.

 2. sani ayasi gololo Avatar
  sani ayasi gololo

  Allah yasaka maka da alkhairi azamanto gdn aljannah ce makomarka

 3. kai yan izala akwai karya da yabon kai. babu mamaki tunda aqidarsu ta samo asali daga aqidar yahudu masu girman kai cewa sun fi kowa yin daidai alhali karya suke yi. yan izala kunce baku jure ma ana saba ma allah da manzo alhali kun fi kowa tabka taasa. ku aka sani da zina da matan aure da sunan karatu. kunfi kowa cin hanci da wawuran dukiyar jamaa kamar wada kuka koya daga gidan sarautan wahhabiyawa na saudiyya masu kwashe kudin petur suyi turai da america suyi ta sharholiya, sauran abinda ya rage a tura ma miyagun mutane kamarku da yan boko haram su yi ta kashe mazan musulmi su kama matansu suna zina da su. ku sani musulmi sun gaji da mugunyar aqida irin taku.

  1. Bello Avatar
   Bello

   Amma yahaya allah yatsinema

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: