TSARKAKE BAUTA

·

·

Domin neman ƙarin bayani danna nan

‘Yan’uwa Musulmai Masu Girma ku kula sosai, addinin musulunci addini ne mai sauki, kuma addinin rahama ne, wadda tazo mana ta hannun fiyayyen halittan Allah, tsarkakakke… Anturoshi domin ya isar da sakon Allah cikakkiya, ya kuma isar cikakkiya bai rage komai ba.. babu wata alkhairi ko sharri wadda annabinmu(saw) bai sanar damu ba.. Babu wata ibada wadda bai nuna mana yadda zamuyi ta ba…. Babu wani manzo da zai sake zuwa bayansa, ku tabbata duk bautan da zakuyi tanada asali daga annabi(saw).. Kada ka fara wani bauta face kana da dalilin yinta, kuma dalilin tazamto daga Qur’ani ko hadisi ingatacce. Daga cikin ibadoji da suka shafi sallah,azumi,zikiri,hajji, da sauransu duka sai da annabi(saw) ya koya mana yadda zamuyishi,duk wani zikiri da kaga sai an jikkata, an firgice, hankali ya fita daga jikin mutum, ido ya fito kuru kuru, toh wannan ba zikirin annabi bane….. inkana son tsira kada ka yadda kayisu sai ta tsarin da annabi(saw) ya koyar. Domin inhar ka tsaba wa tsarin Annabi toh ka halaka. Domin Allah(swt) yace: ‘MASU TSABAWA ANNABI SUJI TSORON KADA WATA FITINA TA SAMESU KO WATA AZABA MAI RADADI’ sai ku kula ku tsarkake bautarku kada ku kirkiri bid’oi domin sai ku halaka… Saboda soyayya da annabi(saw) yake mana mu al’ummarsa saida yayi mana bayaani ya tsoratar damu kan mu tsaya kan tafarkinsa… Yace: ‘duk wadda ya kirkiri wani abu ya sanya cikin wannan addini wadda wannan abun baya cikinsa toh an mayar masa’ toh kunga anan duk wadda zaizoda wani abu mai suna bauta dolene ya kawo hujjah daga mabubbuga mai inganci. Sannan kada ya zama hujjarka shubuha ce. Duk wata bauta da akace maka kayi kaga ana kafa maka hujjah da shubuha toh ka kauce wa wannan hanyar….. ‘Yan’uwa Musulmai mu tsaya cak inda annabi ya tsayar damu, kada muje gaban Allah yana tambayarmu dalili mukasa kawowa… Mukauce wa bid’ah domin Bid’ah tana Halakarwa.. Bid’ah ita ta rusa addinin yahud da nasara, kada muma muyi wasa ta rusa mana namu… Yaa Allah ka kiyayemu… Ka nuna mana Gaskiya Gaskiyace Ka Bamu ikon Binta, Ka Nuna Mana Karya Karyace Ka Bamu Ikon Kauce Mata..

Leave a Reply

Latest updates
Categories