Huduba Daga Mumbarin Masjidu-Tauhid, Ain-shams,AlQahira, Misr(Nibras Muhammad)

Danna nan domin shiga karatu Online

Huduba Daga Mumbarin Masjidu-Tauhid, Ain-shams,AlQahira, Misr.
Bismillahirrahmanirraheem.
Ga Kadan daga cikin abinda yau Khudubar Masjiduttauhi ta kunsa.
Malam Yayi maganane akan Mahimmancin Hadin Kan Musulmai aduk inda suke, sannan ya nuna mahimmancin yin amfani da shari’ar Allah, A kuma kaurace wa duk wata shari’ah wadda bata Allah ba, kaman demokradiyyah da sauransu, Ya nuna cewa addinin musulunci addini ne cikakkiya wadda bata neman wata kari daga ko’ina ya kawo fadin Allah(subhanahu wata’ala)
ﺍﻟﻴﻮﻡ ﺃﻛﻤﻠﺖ
ﻟﻜﻢ ﺩﻳﻨﻜﻢ ﻭﺃﺗﻤﻤﺖ ﻋﻠﻴﻜﻢ ﻧﻌﻤﺘﻲ ﻭﺭﺿﻴﺖ ﻟﻜﻢ
ﺍﻟﺈﺳﻠﺎﻡ ﺩﻳﻨﺎ.
A yau Nã kammalã
muku addininku, Kuma Nã cika
ni´imaTa a kanku, Kuma Nã
yarda da Musulunci ya zama
addini a gare ku.
Sabida haka bai dace musulmai su fice daga cikin da’irar addininsu ba suje wani wuri dabam su nemi wata shari’a wadda zasuyi amfani dashi bata musulunci ba, domin ita shari’ar musulunci itace shari’ah wadda zata gyara duniya a zauna lafiya. Domin ita wannan shari’ah ba mutum bane ya kirkireta, Allah ne ya shimfida ta, shi ya haliccemu kuma yafimu sanin kanmu, shi ya halicce duniya kuma ya fimu sanin me ke cikinta kuma ya fimu sanin me zai kawo gyara acikinta, sabida haka inhar anaso a sami zaman lafiya toh dolene a koma ayi aiki da shari’ar Allah.
Sannan yaja hankali sosai ga ‘yan’uwa musulmai cewa su cire bambance banbance dake tsakani na yare ko wani abu dabam, domin wanda yafi kowa awurin Allah shine wadda yafisu tsoronsa,
Sannan ya cigaba da cewa Ya dace musulmai su dawo suyi riko da addininsu ba addini irin ta Lebral, ko almaniya kodai wasu daga cikin hanyoyi batattu ba, a dawo ayi riko da littafin Allah da hadisai, yace Annabi(sallallahu alaihi wasallam) yace: ‘NABAR MAKU ABUBUWA GUDA BIYU MASU NAUYI, INKUKAYI RIKO DASHI BAZAKU BATA BA HAR ABADA’ SUNE LITTAFIN ALLAH DA SUNNAR ANNABI’. Daga Karshe yayi wa kasar masar da sauran kasashen Musulmai addu’ah ta alkhairi… Allah saka masa. Wannan kadanne daga ciki kashi dari na khuduban Allah bamu daman aiki da abinda mukaji. Ameeen.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates