Mas'alolin Azumi(1)Meye Ma'anar Azumi A Lugga Da Shari'a? Meye Hukuncin Azumin Watan Ramadan? Falalar Azumi.

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Mas’alolin Azumi(1)Meye Ma’anar Azumi A Lugga Da Shari’a? Meye Hukuncin Azumin Watan Ramadan? Falalar Azumi.
Bismillahirrahmanirraheem.
Yabo da Godiya sun Tabbata ga Allah madaukakin sarki, muna neman tsarinsa da kuma gafararsa, Allah nake roko ya bani daman Fadin daidai,
Kaman yadda kuka sani ne zamu fara magana kan abinda ya shafi azumi insha’Allah….
Da farko menene azumi? A Lugga da kuma shari’a?
Azumi a Lugga= shine kamewa, ya game kamewa ga barin cin abinci ne ko kuma ga barin Magana, Da sauransu. Kamar Yadda Allah yace a ayah ta 26 cikin surat maryam.
ﻓﺈﻣﺎ ﺗﺮﻳﻦ ﻣﻦ
ﺍﻟﺒﺸﺮ ﺃﺣﺪﺍ ﻓﻘﻮﻟﻲ ﺇﻧﻲ ﻧﺬﺭﺕ ﻟﻠﺮﺣﻤﻦ ﺻﻮﻣﺎ
ﻓﻠﻦ ﺃﻛﻠﻢ ﺍﻟﻴﻮﻡ ﺇﻧﺴﻴﺎ
To, idan
kin ga wani aya daga mutãne,
sai ki ce, ´Lalle nĩ, na yi
alwãshin azumi dõmin Mai
rahama sabõda haka bã zan yi
wa wani mutum magana ba.
Ma’anar Azumi a shari’ah=shine Kame Baki ga barin Duk abinda zai keta makoshi na abinci ko abinsha, daga bullowan alfijir ta biyu, zuwa faduwan rana, da niyyar bauta wa Allah. Akwai abubuwa da dama masu karya azumi zanyi bayaaninsu nan Gaba,
Meye Hukuncin Azumin Watan Ramadan?
Amsa= Hukuncin Azumin Ramadan Wajibi ne akan duk wani baligi mai iko, kuma duka musulmai sunyi imani da haka, duk wadda yayi inkarin haka toh ya kafirta, fiqhussunnah(1/366).
Allah(subhanahu wata’ala) yana fada cikin surat bakara ayah ta 183
ﻳﺎ ﺃﻳﻬﺎ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﺁﻣﻨﻮﺍ ﻛﺘﺐ ﻋﻠﻴﻜﻢ ﺍﻟﺼﻴﺎﻡ ﻛﻤﺎ ﻛﺘﺐ
ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻣﻦ ﻗﺒﻠﻜﻢ ﻟﻌﻠﻜﻢ ﺗﺘﻘﻮﻥ.
Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni!
An wajabta(1) azumi a kanku
kamar yadda aka wajabta shi a
kan waɗanda suke daga
gabãninku, tsammãninku, zã ku
yi taƙawa.
Sannan kuma da ayah ta 185
ﺷﻬﺮ ﺭﻣﻀﺎﻥ ﺍﻟﺬﻱ ﺃﻧﺰﻝ ﻓﻴﻪ ﺍﻟﻘﺮﺁﻥ ﻫﺪﻯ
ﻟﻠﻨﺎﺱ ﻭﺑﻴﻨﺎﺕ ﻣﻦ ﺍﻟﻬﺪﻯ ﻭﺍﻟﻔﺮﻗﺎﻥ ﻓﻤﻦ ﺷﻬﺪ
ﻣﻨﻜﻢ ﺍﻟﺸﻬﺮ ﻓﻠﻴﺼﻤﻪ ﻭﻣﻦ ﻛﺎﻥ ﻣﺮﻳﻀﺎ ﺃﻭ ﻋﻠﻰ
ﺳﻔﺮ ﻓﻌﺪﺓ ﻣﻦ ﺃﻳﺎﻡ ﺃﺧﺮ ﻳﺮﻳﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻜﻢ ﺍﻟﻴﺴﺮ
ﻭﻟﺎ ﻳﺮﻳﺪ ﺑﻜﻢ ﺍﻟﻌﺴﺮ ﻭﻟﺘﻜﻤﻠﻮﺍ ﺍﻟﻌﺪﺓ ﻭﻟﺘﻜﺒﺮﻭﺍ
ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﻣﺎ ﻫﺪﺍﻛﻢ ﻭﻟﻌﻠﻜﻢ ﺗﺸﻜﺮﻭﻥ.
Watan Ramalãna ne wanda aka
saukar da Alƙur´ãni a cikinsa
yana shiriya ga mutãne da
hujjõji bayyanannu daga
shiriya da rarrabħwa. To, wanda
ya halarta daga gare ku a
watan, sai ya azumce shi, kuma
wanda ya kasance majinyaci ko
kuwa a kan tafiya, sai ya biya
adadi daga wasu kwanuka na
dabam. Allah Yana nufin sauƙi
gare ku, kuma ba Ya nufin
tsanani gare ku, kuma dõmin ku
cika adadin, kuma dõmin ku
girmama Allah a kan Yã shiryar
da ku, kuma tsammãninku, zã
ku gõde.
Cewa da Allah yayi acikin ayah ta 185 (Ya Azumceshi) wannan umarni ne, kuma umarni na wajibi,
Sannan Ankarbo hadisi daga ibn umar(radiyallahu anhu) yace, manzon Allah(sallallahu alaihi wasallam) yace: ‘An Gina Musulunci kan abu biyar,
1.Shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah,Muhammadu Manzon Allah ne,
2.Tsaida Sallah,
3.Bada zakkah,
4.Hajji,
5.Azumin wata ramadan.
Falalar azumin watan ramadan= Azumin watan ramadan yana da falala sosai, ankarbo hadisi daga abu huraira(radiyallahu anhu) yace: manzon Allah(sallallahu alaihi wasallam) yace:’duk wadda yayi azumin watan ramadana yana mai imani da kuma Neman lada awurin Allah anyafe masa duk zunubansa da suka gabata,
Bukhari(4/115/1901).
Ankarbo wata hadisin daga Sahal Ibn sa’ad yace, Manzon Allah(sallallahu alaihi wasallam) yace: ‘A aljannah akwai wata kofa da ake ce mata rayyan, masu azumi zasu shiga aljannah daga wannan kofan, babu wani wadda zai shiga ta wannan kofan saisu, za’ace inaa masu azumi? Sai su taso,babu mai shiga saisu, idan suka gama shiga sai a kulle kofan, babu wadda kuma zai sake shigha daga ta wurin.
Sunan nisa’I(4/167)…
Zamuci Gaba Insha’Allah. Wabillahittaufeeq.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

4 responses to “Mas'alolin Azumi(1)Meye Ma'anar Azumi A Lugga Da Shari'a? Meye Hukuncin Azumin Watan Ramadan? Falalar Azumi.”
  1. abubakar ismaeel funtua Avatar
    abubakar ismaeel funtua

    Ramadan(fasting)

  2. abubakar ismaeel funtua Avatar
    abubakar ismaeel funtua

    Allah yasa mudace!!

  3. Marwan B. Kabir Avatar

    Allah Ya Nunamana Watan Azumin Ramadan Ameen

  4. Salisu h Avatar
    Salisu h

    Allah yasaka da alheri

Leave a Reply

Latest updates
Categories