Tunatarwa Ga 'yan'uwa Musulmai(Nibras Muhammad)

·

·

Kullum su Maqiya addinin
musulunci Bukatansu shine su
dagawa musulmai hankali don
musulmai su tada rikici! Daga
Karshe ace musulmai sun fiye
rikici, ya dace ‘yan’uwa su fahimci
haka… Murinkayin komai bisa
tsanaki da dalili. Wannan dabi’ah
ce tasu, su zagi addininmu su zagi
littafinmu su zagi manzonmu.
Amma in ance a fita basu iyawa…
Allah(subhanahu wata’ala) yace: ﻟﻦ
ﻳﻀﺮﻭﻛﻢ ﺇﻟﺎ ﺃﺫﻯ ﻭﺇﻥ ﻳﻘﺎﺗﻠﻮﻛﻢ ﻳﻮﻟﻮﻛﻢ
ﺍﻟﺄﺩﺑﺎﺭ ﺛﻢ ﻟﺎ ﻳﻨﺼﺮﻭﻥ
Bã zã su cũce ku ba, fãce dai
tsangwama. Kuma idan sun
yãƙe ku zã su jũya muku bãya,
sa´an nan kuma bã zã a taimake
su ba…
Sabida haka ‘yan’uwa a hankalta!!!
Lokaci ya wuce da zamu rinka
maida martani da rikici da tashin
hankali. Lokaci ne na a fita ayi
bayaani na dalili don a fahimci
addininmu! In kuka dubi yadda
abubuwa suke tafiya a yawancin
kasashen musulmai zakuga
koyaushe acikin rikici suke, kuma a
kullum ce mana akeyi mu ‘yan
ta’adda sabida meye? Sabida mu
bazamu bari a taba addini muyi
shiru ba, amma ya dace a kullum
kafin mu dau mataki mu sanyashi a
mizani na shari’ah tukunna da
hakane insha’Allah zamu sami
mafita. Mu kuma sami daman
gamsar da duniya sahihancin
wannan addini tamu ta musulunci
da irin zaman lafiya dake kunshe
acikinta.. Allah mun rokeka ka
daukaka musulunci da musulmai.
Allah ka karemu da sharrin makiya!
Allah ka kawo zaman lafiya aduk
kasashen musulmai da ake fama
da tashin hankali.

2 responses to “Tunatarwa Ga 'yan'uwa Musulmai(Nibras Muhammad)”
  1. Marwan B. Kabir Avatar

    Ameen Ya Allah

  2. Ammen dan uwa

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: