Batun sace yara Almajirai 21 da Canza musu Addini

Yanzu da ace wa’innan Yara 21 Musulmai da aka samesu a garin Jos wanda aka sace su, aka mayar dasu Kiristanci da ƙarfi, Da’ace Kiristoci akayi wa haka da Kaji ko ina ya ɗau ɗumi, da manya manyan ƴan siyasanmu sunyi ta yin Allah wadai.

Amma da yake Musulmai ne Baka jin wani labari akansu, Jaridun da suka kawo labarin ma ɗaiɗaiku ne.

Masu Rajin kare haƙƙin Dan Adam sunyi shiru baka jinsu. Wannan yake nuna mana cewa Dole muma mu tashi domin kare muradun mu, Muyi ƙoƙari wurin buɗe gidajen jaridu, Sannan Idan irin wa’innan abubuwa suka faru muyi iya ƙoƙarin mu wurin yaya ta shi don duniya suji kamar yadda suma sukeyi.

Da yawa wasu ma basu ji labarin ba, sabida mafi yawan Gidajen jaridu da rediyo idan irin wannan abu ya faru da ya shafi musulmai basu cika kawo rahotonsa ba sabida tsabar son zuciya da rashin Adalci.

kowa yasan abinda ya faru lokacin rikicin Deborah da ta zagi Annabi, yadda aka rinƙa yayata maganar kaman ƙasar zata tashi. Ko ina ya ɗau ɗumi Har fadar shugaban ƙasa. Sabida ita Kirista ce.

Sannan Lokaci yayi da iyaye zasu farga su gane cewa wannan zamani ba zamani bane na tura yara Almajiranci. Kowani zamani da abinda ya dace dashi. Tura yaronka zuwa Almajiranci a wannan zamani kaman tura shi zuwa ga Halaka ne. Yaronka zai iya karatun Alqur’ani a Gida, ba dole sai ya tafi wani gari ba.Ya kamata mu zamto masu hankali, mu sani cewa kiwo ne Allah ya bamu kuma Allah zai tambayemu kan wannan kiwo da ya bamu.

Click Here to Support our work

Leave a Reply

%d bloggers like this: