CIN ZARAFIN DA MAKIYA ADDININ ALLAH SUKEYI WA MUMINAI.

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Bismillahirrahmaanirraheen.
ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ ﺍﻟﻢ.
2.ﺃﺣﺴﺐ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺃﻥ ﻳﺘﺮﻛﻮﺍ ﺃﻥ ﻳﻘﻮﻟﻮﺍ ﺁﻣﻨﺎ ﻭﻫﻢ ﻟﺎ
ﻳﻔﺘﻨﻮﻥ.
Ashe, mutãne sun yi zaton a
bar su su ce: “Mun yi ĩmãni,”
alhãli kuwa bã zã a fitine su
ba?.
ﻭﻟﻘﺪ ﻓﺘﻨﺎ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻣﻦ ﻗﺒﻠﻬﻢ ﻓﻠﻴﻌﻠﻤﻦ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺬﻳﻦ
ﺻﺪﻗﻮﺍ ﻭﻟﻴﻌﻠﻤﻦ ﺍﻟﻜﺎﺫﺑﻴﻦ.
Kuma lalle Mun fitini waɗanda
ke a gabãninsu, dõmin lalle
Allah Ya san waɗanda suka yi
gaskiya, kuma lalle Ya san
maƙaryata.
A hakikanin Gaskiya babu yadda za’ayi ya zamana kana kan gaskiya, kana riko da
addinin Allah sau da kafa sannan kayi tunanin ba za’a tsangwameka ba. Domin wannan itace sunnar Allah a bayan kasa.
In muka duba tun farkon fari lokacin annabi adam(as). Tsakaanin yaransa guda biyu zaku dubi yanda Allah ya jarrabi daya daga cikinsu wanda har ya kai ga dan’uwansa ya kashe shi. Toh haka abin zaici gaba da tafiya Har zuwa karshen duniya baki daya.
Sannan ku dubi yanayin gwagwarmaya da annabi(saw) yayi a lokacinsa da makiya gaskiya, haka nan magabata ma suka fafata irin wannan gwagwarmaya, toh haka abin zata cigaba da afkuwa har zuwa ran da zamubar duniyar baki daya. Wato ina irin wannan rubutun ne domin ‘yan’uwa da Allah yake jarrabansu su fahimta cewa hakan ba wani sabon abu bane, kuma basu bane farau.
Wato abin akwai bakin ciki da kuma tashin hankali, abubuwa da suke faruwa kodai akaina ko akan ‘yan’uwa musulmai. Kuma hakan wallahi kara min imani yakeyi sosai, domin ayoyi ne suke gaskatuwa da faruwar irin wannan abubuwa… Kadan daga cikinsu: a yanzu musulmi a nigeria ya inhar zaiyi shiga ta musulunci toh wallahi ya zama abin zargi, kwanakin baya akan hanyaata ta tafiya, aka tsayar damu a wurin bincike na jami’an tsaro, amma abin mamaki irin bincike da akayi wa wa’inda ake ganinsu da tufafi irin ta musulunci tasha bambam da wanda ake wa wa’inda sukayi shiga irinta yahudu. Haka inka duba a wasu wurare akeyi,sannan abinda ya kara tada min hankali shine: jiya wani abokina sukaje daurin aure a bauchi. A hanyarsu ta
dawowa aka tsaresu a wani wurin binciken ababen hawa, abin mamaki ana barin kowa ya wuce sai ga wata mota mai dauke da wani malami mai almajirai, sai aka tsare wannan malami dashi da almajiransa, aka fitar dasu baki daya, aka fara tuhumarsa tuhumar da ba’ayi wa wasu irinta awurinba, yayi musu bayaanin cewa shi daga jahar jigawa yake kuma zai je jahar pilato ne domin cin rani da kuma karantar da almajirai kamar yadda suka saba. Amma haka jami’an tsaron nan suka ki amsar wannan bayaani na wannan malamin zaure, abinda jami’in tsaron yace masa shine; ‘kana daukan yara kaje ka koya musu boko haram ko?’ Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un. Shin dun Allah irin wannan zance ya dace ya fito daga bakin mai ikrarin kare mutane?.. Toh da ire iren wa’innan abubuwa ya zama wajibi ‘yan’uwa mutashi muyi karaatu domin kwato hakkinmu. Kuma musulmai masu aikin hukuma suna da wata gudumawa da zasu iya bada wa a wannan fage… Allah ya taimake musulunci da musulmai, ya karya kafirci da kafirai. Ya ruguza ta’addanci da ‘yan ta’adda.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

2 responses to “CIN ZARAFIN DA MAKIYA ADDININ ALLAH SUKEYI WA MUMINAI.”
  1. aminu Saad Avatar
    aminu Saad

    Allah ya tsinemawa kafurai

  2. メンズ水着 迷彩

Leave a Reply

Latest updates
Categories