Koyi Da Yahudu Da Nasara Bala'i ne

·

·

Assalaamu Alaikum ‘yan’uwa musulmai. Da yawa daga cikin ‘yan’uwa musulmai suna ruduwa da tsarin rayuwa irin na yahudu da nasaara, wanda a zahiri inka dubi irin wannan rayuwa ta yahudu da nasara cike take da hatsari da kuma bala’I. A hakikanin gaskiya a duniyance in muka dubi yanayin rayuwarsu zaka samu abinda bincikenmu zai bamu shine cewa suna cikin rayuwa mai dadi, wanda har suna zama abin koyi. Toh ‘yan’uwa a hakikanin gaskiya duk ranar da wani ya tsinci kansa kan wannan tunani ta yin koyi da yahudu da nasara toh ya tabbata yana dab da fadawa ramin halaka. Allah ya karemu…
Da farko Allah ya fada mana cikin surah ta 3 ayah ta 112
ﺿﺮﺑﺖ ﻋﻠﻴﻬﻢ ﺍﻟﺬﻟﺔ ﺃﻳﻦ ﻣﺎ ﺛﻘﻔﻮﺍ ﺇﻟﺎ ﺑﺤﺒﻞ ﻣﻦ
ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺣﺒﻞ ﻣﻦ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻭﺑﺎﺀﻭﺍ ﺑﻐﻀﺐ ﻣﻦ ﺍﻟﻠﻪ
ﻭﺿﺮﺑﺖ ﻋﻠﻴﻬﻢ ﺍﻟﻤﺴﻜﻨﺔ ﺫﻟﻚ ﺑﺄﻧﻬﻢ ﻛﺎﻧﻮﺍ
ﻳﻜﻔﺮﻭﻥ ﺑﺂﻳﺎﺕ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﻳﻘﺘﻠﻮﻥ ﺍﻟﺄﻧﺒﻴﺎﺀ ﺑﻐﻴﺮ ﺣﻖ
ﺫﻟﻚ ﺑﻤﺎ ﻋﺼﻮﺍ ﻭﻛﺎﻧﻮﺍ ﻳﻌﺘﺪﻭﻥ.
An dõka ƙasƙanci a kansu a
inda duk aka sãme su fãce da
wani alkawari daga Allah, da
alkawari daga mutãne. Kuma
sun kõma da fushi daga Allah,
kuma aka dõka talauci a kansu.
Wannan kuwa dõmin sũ, lalle
sun kasance suna kãfirta da
ãyõyin Allah, kuma suna kashe
annabãwa, bã da wani haƙƙi ba.
Wannan kuwa dõmin sãɓãwar
da suka yi ne, kuma sun
kasance suna yin ta´adi.
Toh kaman yanda kukaji Allah ya fadi acikin wannan ayah toh haka wannan kaskanci take kansu har zuwa ran tashin qiyaama. Sai dai wanda yayi imani daga cikinsu kama yanda Allah ya kara bayaani a gaba. Yace:
ﻟﻴﺴﻮﺍ ﺳﻮﺍﺀ ﻣﻦ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﺃﻣﺔ ﻗﺎﺋﻤﺔ ﻳﺘﻠﻮﻥ
ﺁﻳﺎﺕ ﺍﻟﻠﻪ ﺁﻧﺎﺀ ﺍﻟﻠﻴﻞ ﻭﻫﻢ ﻳﺴﺠﺪﻭﻥ.
Ba su zama daidai ba; daga
Mutãnen Littafi akwai wata al
´umma wadda take tsaye, suna
karãtun ayõyin Allah a cikin sã
´õ´in dare, alhãli kuwa sunã yin
sujada.
Toh wa’innan ne kawai suke cikin
natsuwa. Ku dubi yanayin kasashen turai yanzu kullum acikin tashin hankali suke
kullum acikin kere keren makamai suke saboda baki daya hankalinsu ta kasa kwanciya. Ku dubi isra’ila yanzu wallahi palastinawa duk da cewa an mamayesu amma sunfi isra’ila kwanciyar hankali, sannan abinda yasa da yawa kuke ganin turawa suke zuwa bakin ruwa, da hawa jirgi domin zuwa sama jannatii, da yawaita zuwa gidan zoo. Ba komai bane sai don kawai rashin kwanciyar hankali da kuma rashin samun abinda zai kwantar musu da hankalin. Shi yasa zaka gansu kullum a irin wa’innan wurare, amma a matsayinka na musulmi Allah ya baka abubuwa da zai sanya maka natsuwa. Ga karatun qur’ani, ga zikiri. Ga kuma natsuwa ta cewa kana kan addinin gaskiya mai dalili. Toh meye naka na koyi da irin wa’innan mutane wanda ga abinda Allah ya fada akansu?
Sannan ‘yan’uwa daga jiya zuwa yau masu ganin kafafen yada labarai da kuma karantawa sunga labarin wani matashi da ya kashe iyayenshi, da kuma kanaanan yara a kasar amurka a garin’ Newtown’ jiya. ku tambayi kanku ‘yan’uwa me yake jawo musu irin wannan abu? Domin wannan ba shine farau ba kunsani, a watannin baya ma a faransa anyi haka. Toh hakikanin gaskiya wannan ayah da ta gabatace kawai take gaskatuwa akansu. Sannan kuna nufin yanda turawa suke zuwa su mamaye kasahen musulmai inda kasashensu ne ake zuwa a mamaye da ba dukansu sai sun zama ‘yan kunar bakin wake ba? Saboda haka dai ‘yan’uwa a kula, in kuna neman cikakkun ‘yan ta’adda toh sune yahudu da nasaara, kuma bai dace ayi koyi dasu ba ko ta wata hanya.
Inkanaso kayi koyi kayi koyi da annabi, komai yazo mana dashi. Sanya tufafi,soyayya,zance, da duk koma meye, in soyayya kakeso ka koya, shiga hadisan manzon Allah zaka zama prof a harkar soyayya, amma da zarar ka dauki tsarin soyayyar yahudu da nasara toh wallahi mutum yana da halaka. Haka sanya tufafi yi koyi da annabi sai kaga kafi jin dadi kuma ka sami lada. Amma da zarar kayi koyi da yahudu da nasara wurin sanya tufa, kana sanya wando kana barin al’auranka a waje da sunan ‘ass down’ toh kana dab da halaka. Allah ya kiyayemu. Kuma ‘yan’uwa ku sani yin koyi da annabi cikin komai namu shine samun zaman lafiyarmu, wannan kawai misali na kawo. Allah ya karemu Ya kuma dada shiryar damu. Subhanakallahumma wabihamdik, nastagfiruka wa na tubu ilaik.

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: