Adalci wa Ahlussunnah(Muhammad Rabi'u Rijiyar Lemo)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Wannan Batu Haka Yake
Masu hikimar zance sukan ce
“Mutum makiyin abin da bai sani
ba ne”. Babu ko shakka duk wanda
ya kalli mafi yawan masu fada da
Ahlissunnah, zaka gansu suna
fadan ne akan jahiltar hakikanin
tsarin (wato manhajin)
Ahlissunnah, wanda aka gina shi
akan ilimi gaskiya da adalci, mafi
yawansu suna dogara ne akan
abin da munanan malami suka
fada musu, ko kuma a kan wasu
dabi’u da ta’adu na jahilan
Ahlissunnah.
Alal misali idan mutum ya dauki
bajimin malamin nan na sunnah,
shahararre mai dimbin sani,
shehun musulunci Ibnu Taimiyyah,
zai ga da yawa daga cikin masu
zaginsa da kafirta shi da munana
shi, basu san komai a kan tarihinsa
ba, basu karanta littattafansa ba,
kawai suna daukar abin da
makiyansa suka rubuta a kanshi na
karya da taawilin maganganunsa
su shiga yadawa da jayayya a kai,
amma duk wanda yake karanta
littattafansa da idon basira zai yi
mamakin irin adalci da tausasa da
fadin gaskiya na wannan bawan
Allah, Allah ya jikan wani
malaminmu a Jami’ar Musulunci ta
Madinah, ya kasance yana cewa,
“Mafi yawancin mutane suna
karanta littattafan Ibnu Taimiyyah
amma basa daukar ladabinsa da
halayensa” Don haka dan uwa
zama mai adalci wajen yin hukunci
ga wani mutum ko kungiya ko
wasu mutane, karanta abin da
suka rubuta da kansu, koma cikin
jiga-jigan littattafansu, tana nan ne
zaka gane gaskiya, Allah ya raba
mu da son zuciya.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

7 responses to “Adalci wa Ahlussunnah(Muhammad Rabi'u Rijiyar Lemo)”
 1. Iliya ibn aliyu Avatar
  Iliya ibn aliyu

  Toh masha Allah da kasan mutum makiyine akan abunda ya jahilta.kuma ance ko wani tsuntsu kukan gidan su yakeyi, barewa baza tai guduba ya,yanta suyi rarrafe. Toh kunsan haka meyasa kuke gahba da darikun sufaye? Domin masu dariku walliyai ne jikokin annabi muhammad(S.A.W) ya za ayi wani bawan Allah kamar ibn taimiyya yafi Ahmadu tijjani ko Abdulqadir jillani kyawawan dabi,a da ilimi??
  Ahmadu tijjani dan
  1.muhammad
  2.mukhtar
  3.ahmad
  4.muhammad
  5.salim
  6.abil eid
  7.salim
  8.ahmad
  9.ahmad
  10.aliyu
  11.abdullahi
  12.abbas
  13.abduljabbar
  14.idris
  15.idris
  16.ishaq
  17zainul_abideen
  18ahmad
  20.muhammad nafs zakiya
  20.abdullah kameel
  21.hassan musannan
  22.imam hassan
  23.imam ali
  24.fatimatu zahara
  25.ANNABI MUHAMMAD(S.AW). Kunji tushensa haka abdulqadirma yake.
  Dan haka waye ibn taimiyya?

 2. Iliya ibn aliyu Avatar
  Iliya ibn aliyu

  Allah yasa mu dace yashirda musulman xamani yan addinin shekara 35 su dawo su hadu da yan uwansu musuluman kasannan yan shekara 927

 3. - MS SHARIFAI Avatar
  – MS SHARIFAI

  Wannan haka yake!
  Adalcin ne ya sa muke son ku rinka karanta abin da yake rubuce a cikin ‘Sitta sahih’ naku, musamman ‘BUKHARI DA MUSLIM’, don ku fahimci gaskiyar abin da ake gaya muku game da wadansu daga cikin wadanda ake kira da sunan wai SAHABBAI!!!

 4. - MS SHARIFAI Avatar
  – MS SHARIFAI

  GAME DA DAN TAIMIYYA KUWA:
  Har abadan abadan ba zamu ga kimar duk wanda ya bude wawwaran bakinsa ya soki tare da zagin TSARKAKA KUMA MA’ASUMAI BAYIN ALLAH KAMAR IMAM ALIYU DA NANA FADIMA a.s., ba! Musamman irin shi wannan da ake kira da Dan Taimiyya.

  1. Iliya ibn aliyu Avatar
   Iliya ibn aliyu

   Abokina kyale su dai ai mu tuni mungane sune makiya Annabi ne da yayansa tunda basu kaunar suji an ambacesu ko kadan kamar su imam khomaini,jillani,tijjani da sauransu. ALLAH YA LA,ANCI YAZIDU da Makarabansa dakuma masoyansa

 5. Salisu h Avatar
  Salisu h

  Allah yasaka

 6. - MS SHARIFAI Avatar
  – MS SHARIFAI

  Amin ‘yan uwa.

Leave a Reply

Categories
Latest updates