Bama yin kira zuwa ga Theocracy

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Mai Rubutu: Hamza Diso


Tun a ƙarni na ɗaya aka fara amfani da kalmar Theocracy don yin ishara zuwa ga Hukumar yahudawa wadda aka gina ta bisa doron Addini zalla, wanda wannan ya saɓawa dukkanin nau’ikan daulolin da girkawa suka sani a wancan zamani. Ance mutum na farko daya fara amfani da wannan kalmar shine josephus Flavius.

  Sai dai maganar gaskiya itace akwai dauloli dayawa da akayi akan wannan tsarin tun kafin yahudawa da kuma bayansu, kamar daular tsohuwar Masar da indiya da makamantansu.
Ko su kansu yahudawan yanayin daular yana sauyawa a wajen su daga zamani zuwa zamani , misali yanayin tafiyar da daular a zamanin Alƙalai yana da banbanci da zamanin sarakuna da kuma lokacin Annabawa. Haka kuma ba zaka iya yiwa waɗannan dauloli hukunci guda ɗaya ba, saboda ita daular addini mutane ne suke jagorantar ta ba Mala’iku ba saboda haka gwargwadon kirki da Adalci da iya jagorancin da shugaba yake dashi gwargwadon hukuncin da za ayi wa wannan daular. Wannan shi yasa zaka iya tsintar daular yahudawa a wasu zamanin cikin lalata da shirme da kama karya kamar yadda wasu daga cikin ƴaƴan Annabi sulaiman sukayi har suka raba daular gida biyu, da abubuwan da suka biyo bayan hakan

To amma abin tambaya anan shine ina matsayar musulmi akan irin wannan daular?
Sanannan abune a gurin duk wanda yake da kwalli a ido cewar shi musulunci addini ne daya haɗa duniya da lahira, jiki da ruhi to amma fa baya bawa jagororin daularsa damar su mallaki mutane da sunan Allah wato kayan Allah nasu ne, ko ace jagorori suna da wani tsarki na daban wanda sauran mutane basu dashi.

Shi shugaba a musulunci mutum ne kamar kowa yana iya dai-dai yana iya kuskure kuma al’umma suna da haƙƙi akansa na ya kare musu addinin su da rayuwar su da lafiyarsu da duk abinda zasu buƙata. Maganar sa ba wahayi bace saboda haka idan yayi kuskure za ayi masa gyara, shi yasa Khalifa Abubakar yace ” idan nayi kuskure to ku dai-dai tani,” kuma bashi da haƙƙin yin wani gagarumin abu ba tare da jin ra’ayin masu hankali cikin Al’umma ba.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories