NEW ATHEISM ( SABON ILHADI)

·

·

Yana da wahala a iya cewa ga lokacin farko da aka fara Ilhadi a Duniya, amma dai an fara jin motsinsa a Indiya Ɗaruruwan shekaru kafin Haihuwar Annabi Isa lokacin da wasu suka fara yiwa Addinin Gargajiya na Indiya tawaye Sai dai ya bayyana ne a fili a lokacin Buddha ta yadda har masu wannan Aƙida suke gabatar da laccoci a bainar jama’a Harma ana yin sa’insa dasu kamar yadda yazo acikin littafin (The story of Civilization) sanda yake magana akan Lokacin Buddha, Ma’auratan mawallafan suka ce :

“Others demonstrated the Non-existence of God, and the inexpediency of virtue. Large audiences gathered to hear such lectures and debates, great halls were built to accommodate them”

(chap.xv page 418)

Haka shi kansa Addinin Buddha din akwai Nau’in Ilhadi a cikinsa don dayawa daga cikin mabiyan Addini babu Ruwansu da Allah, wannan yasa wasu suke ganin Budanci falsafa ce ba addini ba. Haka anji motsin Ilhadi a Daular farisawa(Persian Empire) da kuma Zamanin Girkawa kamar yadda a kaji motsinsu a kasashen musulmai a wajen irinsu ibnu rawandah Sai dai Ilhadin nasu bana Kore samuwar mahalicci bane kawai dai suna Kore Annabci da kuma wahayi. Amma Ilhadi bai samu Gurin Zama ba Sai da Ya hadu da Communism da Marxism A hannun Yahudawa kamar yadda su Yahudawa suka fada da kansu cewa sune suka ƙirƙiri Marxism acikin (The Protocols of the Elders of Zion) A cikin protocol na 2 sukace:

Ahir dinku ku zaci cewa Abinda nake fada bashi da muhimmanci sosai! Kawai abinda zaku tuna shine abinda muka yi ta Hanyar (ƙirƙiro) da theory din Karl Marx(Wanda ya ƙirƙiri Marxism) da Darwin(Wanda ya ƙirƙiro cewa Dan Adam yabi matakai dayawa kafin ya zama mutum tun daga tsutsa har yakai Biri har ya zama Mutum) da kuma Nietzsche (Wanda ya fadi maganar nan da tayi shura ta cewa Allah ya Mutu)

(Duba shafi na 155 na protocols Wanda aka tarjama zuwa Larabci)

Sai Dai bayan Gama yaƙin Duniya na Biyu Ilhadi yaja da baya kafin yanzu ya sake dannowa da ƙarfi a ƙasashe dayawa musamman da sunan Sabon Ilhadi Shi wannan suna Sabon Ilhadi ana ganin mutum na Farko daya fara Amfani dashi shine Jerry Wolf a shekarar 2006 a wani Rubutu da yayi mai taken (The Church of the Non- Believers) Wanda shi wannan sabon Ilhadi ya shiga guraren dayawa da siffofi kala-kala A haqiqa shi Ilhadi kala uku ne

  1. Atheism (kore samuwar Allah)
  2. Agnosticism ( shakka akam samuwar Allah)
  3. Deism (Akwai Allah amma ba ruwansa da bayi)

A Rubutu na Gaba zan kawo Dalilan yankan shakku akan samuwar Allah da kuma Gaskiyar wahayi da Gaskiyar ƙur’ani da kuma wajibcin Aiki dashiAllah yasa mu dace.

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: