BUKATUWARMU GA TARBIYYA A YAU FIYE DA KOMAI(Muhammad Rabi'u Rijiyar Lemo)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Na san duk mai bibiyar al’amuran
addini a wannan kasa tamu
‘Nigeria’, akan kowacce fahimta
kuwa yake zai yadda da ni wajen
cewa an samu bunkasar ilimin
addini da wayewa fiye da shekara
ashirin baya, a yau akwai matasa
masu yawa da suka gama
karatunsu na addini a ciki da wajen
Nigeria, wadanda akalla suka
samu digiri na farko ko na biyu kai
har ma dana ukun, kuma duk
wanda ya saurare su, ya san cewa
sun sami ido a ilimin addini daidai
gwargwado, haka nan ma a yau
yadda ake karantarwa a kafafen
yada labarai da majalisosi abin sai
godiya, to amma duk da haka
kullum muna ganin sababbin
matsaloli da suke kunnowa,
wadanda ya kamata a ce ci gaban
da ake da shi na ilimi ya yi
maganinsu, amma ina? Lamarin ya
zama jiya a yau!.
Alah hakika a iya dan bincikena da
fahimtata ba wani abu ba ne ya
kawo wannan matsalar face rashin
tarbiyya da muke fama da ita.
Tarbiyya jigo ce a cikin harkan
neman ilimi, a duk lokacin da
dalibai suka shagalta da koyon
karatu amma ba ruwansu da
kwaikwayon tarbiyya da ladabin
ilimi da malamai to za su shiga
bankaura da rashin amfanuwa da
amfanarwa, wannan ya sa
magabatanmu na kwarai suka ba
wannan bangare kulawa, suka
damu da tarbiyantar da dalibansu,
kamar yadda suka damu da koyar
da su ilimi, sai aka wayigari ilimi da
tarbiyya suna tafiya kafada da
kafada, dalibi yana karatu yana
kuma koyon ladabi da tarbiyya,
inda anan ne dalibi yake koyon
tawali’u da kaskantar da kai, da
ikhlasi, da girmama na gaba, da
tausayawa na kasa, hakuri, da son
juna, da rashin girman kai da
dukkan wani hali nagari.
Allah yajikan malumanmu na soro,
wadanda sukan fara koyawa dalibi
littafin Ta’alim kafin komai, kamar
yadda suke koya masa zama
gaban malami, da kaskan da kai,
irin in ace masa malam ya ce
“almajiri dai” da sauransu.
Don haka babu ko shakka akwai
bukatar malumanmu da daliban
iliminmu masu karantawa su
waiwayo wannan bangare, su
bashi mahimmanci, su sanya
littattafan da malamai suka rubuta
akan ladubban dalibin ilimi su
karantar da su, su komawa
kyawawan halayen Manzon Allah
(S.A.W) da yadda ya zauna da
sahabbansa su dabbaka su a
rayuwarsu da dalibansu. Allah ya
yi mana jagora. Ameen.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories