Allah ko Yahwa ko Yesu ko Buddha?

Mai rubutu: Hamza Diso


Mulhidi yakan ce idan ma mun yadda da Allah to wanne ne na gaskiya? Tunda kowanne addini yana kirane zuwa ga Ubangijin wannan addinin kawai!!!

Duk da cewa bai kamata wanda yake da’awar hankali da ilimi yayi wannan tambayar ba, to amma zamu bada amsa saboda isar da hujja ga kowa

Su addinai kala biyu ne, akwai addinin ƙasa akwai na sama

Addinan ƙasa sune addinai na gargajiya waɗanda mutane suka ƙirƙira da kansu kuma fahimtar ɓacin waɗannan addinan bashi da wahala
Misali Buddha Wanda ko ni nasan sunan mahaifiyarsa da shekarar da aka haifeshi da wacce ya mutu tayaya zai zama Allah?

Sannan ga maganganun da ake jingina masa mun riske su, shi kansa baice shi Allah bane baima yi da’awar Annabta ba

Sannan a haƙiƙa buddhanci falsafa ce ba addini bane, don dayawa daga cikin mabiyansa  babu ruwansu da Allah, su kawai suna magana ne akan kyawawan ɗabi’u

Kenan Buddha ba Allah bane bai kuma yi da’awar Allantaka ba, wasu daga cikin mabiyansa ne suke wuce gona da iri wajen girmama shi amma masu hankalin cikin su basu yadda da haka ba

To haka duk sauran addinan gargajiya suke daga masu bautar mutum sai masu bautar dabba ko taurari ko haske ko duhu, waɗannan abubuwan kuwa duk fararru ne ba hankali acikin bauta musu.

Amma addinan sama kamar musulunci da hayudanci da kiristanci, ba rigima suke akan Allah ba

Allah wanda ya saukar da attaura shine ya saukar da Bible da ƙur’ani kuma haka ya faɗa da kansa a ƙur’anin.

To kenan a ina matsalar take??

Attaura littafi ne da aka saukar dashi shekaru masu yawa kafin haihuwar Annabi Isa sai dai a tarihi an rasa ta har sau biyu sai kawai kaji wani ya bayyana yana cewa ya dawo da ita
Wannan yasa bamu yadda da ingancin ta ba ɗora akan haka sauya ma’anoninta dama haruffan ta da malaman Yahudawa sukai tayi,

Kenan matsalar mu da yahudanci manyan abubuwa guda biyu ne

  1. bamu yadda cewa wannan attaura itace wacce Allah ya saukar ba duk da cewa akwai abubuwa dayawa na dai-dai acikin ta. Kuma muna da dalilai masu yawa akan wannan fahimta tamu, sai dai ba wannan ne maudu’in mu ba.
  2. wahayin gaskiya ya sauka ya dakatar da aiki da ita( gaba zamu yi magana akan dalilan gaskiyar wahayin da muke bi).

Kenan ba rigima ce tsakanin Alloli biyu ba kamar yadda mulhidi yake nunawa

Haka kiristanci na gaskiya Allah ne ya saukar dashi zuwa ga yahudawa su kaɗai, wannan ne yasa aka tilasta musu yin amfani da attaura wato itama Kirista sunyi imani da ita barima ɓangare ce mai muhimmanci acikin littafin su
Idan Kirista yace littafi Mai Tsarki yana nufin waɗannan abubuwa

  1. Tsohon Alƙawari(  Old Testament)     littattafan yahudawa wanda cikinsa akwai littattafan Annabi Musa guda biyar (Attaura) da sauran abubuwan da suke da alaƙa da yahudawa.
  2. Sabon Alƙawari( New Testament)  Bible guda huɗu da kuma rubuce-rubuce na mabiyan kiristanci na farko

Su Kiristoci matsalar mu dasu itace

  • sauya ainihin Addinin ta hanyar saɓa wa tsohon Alƙawari dama duk sauran addinan annabawa da suka gabata domin kuwa sun shigar da yesu cikin Allah haka ruhi mai tsarki,
    Wanda hakan ya saɓa wa hankali da kuma wahayi kuma muna da dalilai dayawa akan haka sai dai ba maganar mu kenan ba
  • Bible ɗaya ne ya sauka mu kuma munga guda huɗu wadanɗa coci ta yadda dasu kuma dukkanninsu ba a gaban Annabi Isa aka rubuta ba barima bamu yadda cewa cikin waɗanda suka rubuta akwai ɗalibinsa ba. Sannan akwai bible kala-kala da aka ƙona.
  • Akwai Bible da muke ganin yafi inganci shine Bible ɗin barnaba, shi kuma baya cikin huɗun.
  • Saukar wahayin gaskiya daya soke aiki da Bible.

Kenan ba rigima muke yi akan Allah ba, a’a akan aiki da abinda yake hannun su ne

Shi yasa Allah yace :”lallai mu munyi maka wahayi kamar yadda muka yiwa Nuhu wahayi dama sauran annabawa da suka zo bayansa” Annisa – 163


Allah ya karɓi rayuwarmu muna muminai

Click Here to Support our work

Leave a Reply

%d bloggers like this: