Meyasa muke buƙatar wahayi?

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Mai rubutu: Hamza Diso


Wasu daga cikin masu inkarin addini suna ganin cewa tunda dai Allah ya bamu wadataccen hankalin da muke iya gane dai-dai da kuskure to meyasa kuma zamu buƙaci wahayi?

Sai dai wannan magana tasu bata kan turba, don saboda bayyanar buƙatuwar mu zuwa ga wahayi har sai da wasu cikin masu bin mazhabobin hankali suka zarme sukace wajibi ne akan Allah sai ya turo manzanni, don sai da Koyarwarsu ne rayuwa zata miƙe ɗoɗar.

Duk da cewa sunyi kuskure mai muni wajen wajabtawa mai wajabtawa, to amma fa ɗan Adam lalle yana buƙatar wahayi, ga wasu daga cikin dalilan mu.

1. Abubuwan da zamu iya samun ilimi tasu sun haɗa da hankali, gaɓɓai biyar na samun ilimi da gwaji a dakin gwaje-gwaje (experiment)
Sai dai duk waɗannan hanyoyi sukan bamu matsala wani lokacin

Shin kasan zai yiwu kaga abu da idonka ashe ba haka haƙiƙarsa take ba? Kasan cewa abubuwa masu kala da kake kalla ashe haƙiƙa itace basu da kalar komai, ita kalar a ƙwaƙwalwar ka take ba a jikinsu ba?

Kasan abubuwa da kake ganinsu da tauri a haƙiƙa ba tauri ne dasu ba?

Idan baka san wannan ba to ga mai sauƙi, ai dai kasan cewa wata da rana da kake ganinsu a matsayin ƙanana ashe manya ne.

Ka kuma san cewa idonka da kunnen ka suna da iyakar abinda suke gani ko ji don akwai iya tazarar da bazasu iya dakko abinda ya wuce ta ba.

Haka shima hankali yana da tasa iyakar, wannan shine dalilin da yasa ake samun fifiko a cikinsa, ko kuma kayi amfani dashi ka gano wani abu sai daga baya ka gani ashe shirme kayi, wannan shiyasa irinsu Immanuel Kant suke kira akan adingayiwa shi kanshi hankalin naƙadi kafin a karɓi abinda yazo dashi.

Bamu da shakka akan cewa muna iya samun ilimi ta waɗannan hanyoyi kuma zamu ci gaba da dogara dasu wajen neman sanin abinda bamu sani ba na duniya, wataran muyi dai-dai wataran muyi kuskure.

To amma idan ya zamo Abubuwan da muke gani ko muke rayuwa dasu ma ga yadda muke fama dasu to yaya kuma idan muka zo magana akan (metaphysics) Abubuwan da bama gani bamaji?

Anan dole zamu buƙaci wahayi ya taimaka mana ya ɗora mu a hanya

2. kallon yadda aka halicci duniya akan tsari mai ban mamaki zai tabbatar maka da cewa lallai wanda ya halicce ta mai cikakken iko da hikima ne. Shin kana zaton mai hikima kamarsa zai yi halitta sa sakai ba tare da manufa ba? To idan bata wahayi ba ta ina zaka san manufar halittar?

3. ƴan Adam suna buƙatar kyakkyawan tsarin da zasu bi wajen tafiyar da rayuwarsu akan tsari da Adalci, shi kuma wanda zai yi tsarin da za abi ya kamata ya cika sharudda.

  • ya zamo ya nesanta da son zuciya ta yadda zai yi adalci cikin dokoki sa.
  • ya zamo bai da maslaha dayake buƙatar samu ballantana ya saka dokar dashi kawai zata amfana ko danginsa.
  • ya zamo yana da cikakken ilimin abinda ya wuce da wanda zai zo don ya sanya dokar da zata dace da kowa kuma a ko ina da kuma kowanne zamani.
  • ya zamo baya tsoron kowa kuma baya bukatar wani abu a wajen kowa.
  • ya zamo babu wanda zai iya guje masa ballantana mutum ya karya doka ya gudu wani gurin kuma shi kenan ya tsira har abada.
  • ya zamo yana da girma a zuƙatan mutane ta yadda zasu guji saɓa masa.

Shin kana ganin akwai wanda ya cika waɗannan sharuɗa bayan mai kowa da komai, mai cikakken ikon da ba a iya guje masa, bashi da ɗa ko jika ko mata ko siriki balle kayi kamun ƙafa?

Idan Allah ne kawai zai iya to ai babu hanyar yin hakan sai ta wahayi.

4. ƴan Adam suna buƙatar tsari guda wanda zai haɗa kansu idan suka bishi yadda ya dace, kuma kasan dai babu wanda zai iya saukar da tsarin da zai dace da kowanne yanki sai Allah shi kaɗai

Waɗannan kaɗan ne cikin hujjojin wahayi waɗanda hankali zai iya fahimta
Allah ya datar damu

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories