MATA MASU SHIGA TV DON WATSA LABARAI, KO KARANTAR DA GIRKE-GIRKE KO WA'AZI, KUYI HATTARA DAGA FITINAR DA KU KA AUKAWA(Sheikh Isa Ali Pantami)

·

·

Shaykh Bn Baz (RH) yana cewa
yana daga cikin mafi girman fitina a
wannan zamani, shine yarda
MATA masu garaje da rashin
kamun kai suke shiga cikin TV da
sukan karantarwa bayan basu da
isheshshen ILMI da TARBIYYA ta
ADDINI ko karantar da girke-girke.
Don haka MUSULUNCI ya kawo
ka’idodin kare AL-UMMAH daga
FITINTINU da LALACEWAR
TARBIYYA.
Annabi (SAW) yana cewa: Babu
wata FITINA da na bari a bayana
mai cutar da MAZA fiye da MATA
ba (Bukhari:5096).
Sannan Annabi (SAW) yana cewa:
Kuyi kaffa-kaffa da DUNIYA kuma
kuyi kaffa-kaffa da MATA, saboda
FITINAR farkon ga BANU-ISRAILA
ta kasance a cikin MATA ne
(Muslim: 2742).
Idan muka duba ZAHIRIN
abubuwan da ke faruwa a yau,
zamu kara tabbatar da GASKIYAR
Manzon Allah (SAW) wanda baya
MAGANA akan son rai, sai dai idan
wahayi aka masa.
Bincike ya nuna cewa Kashi 70
zuwa 90 na matan dake aiki,
musamman suke fitowa a kafofin
watsa labarai sun tab’a yin ZINA.
Duba Mujallar Ad-Da’wah no 1783.
MATAN AURE da suke shiga TV
don watsa labarai, ko karantar da
GIRKE-GIRKE, ko hira da yan
jarida ko karantarwa, musamman
ma fuskarsu a bude mafiya yawa
bincike ya nuna 1) Basu da kunya
2) Basu da kamun kai 3) Masu son
a sani ne 4) Basu da karatun
addini amma suna nuna su wasu
ne 5) Masu son daukaka da
burgewa ne 6) Basu da cikakkiyar
biyayya ga mazan aurensu 7)
Masu son mu’amala da maza ne.
Don haka IYAYE MATA, sai kuyi
hattara ku kame kanku da
‘ya’yanku daga wannan FITINA ta
son shiga KAFOFIN WATSA
LABARAI. Ku zauna inda Allah ya
tsayar da ku.
Yaa Allah ka kare mana
ZURIYARMU daga wannan
FITINA,…

3 responses to “MATA MASU SHIGA TV DON WATSA LABARAI, KO KARANTAR DA GIRKE-GIRKE KO WA'AZI, KUYI HATTARA DAGA FITINAR DA KU KA AUKAWA(Sheikh Isa Ali Pantami)”
  1. Ameen malam

  2. zahiri jin tsoron ALLAH AKO INA SHINE MAFITA

  3. Ahmad Avatar
    Ahmad

    Salam, abunda Malan ya fadi gaskia ne, amma menene mafita, mubar yayanmu da matanmu ga turawa don su suka fi yin irin wadannnan abubuwa a TV ko my hana su kallon TV gabadaya?

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: