DABI'UN MUMINI A LOKACIN FITINTINU(Sheikh Isa Ali Pantami)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

DABI’UN MUMINI A LOKACIN
FITINTINU: Allah ka bamu nasara
Duniya da Lahira,…
Annabi (SAW) yana cewa: Kuyi
gaggawan aikata ayyuka (na
alheri), saboda fitintinu zasuyi
yawa kamar yankin dare mai duhu.
Mutum zai wayi gari yana MUMINI,
gabannin YAMMACI kuma ya
zama KAFIRI. Wani kuma zaiyi
YAMMACI yana MUMINI gabannin
GARI ya waye ya zama KAFIRI.
Saboda zai sayar da ADDININSA
don Neman kayan Duniya (Muslim
ya ruwaito).
DABI’UN MUMINI A CIKIN
FITINTINU sune:
1) JURIYA, DA TAUSASAWA DA
BIN ABU MATAKI-MATAKI. Annabi
(SAW) yana cewa: Tausasawa
idan ya shiga komai yana kyautata
shi. Idan kuma aka cire shi a komai
yana lalacewa (Muslim ya ruwaito).
2) TAQWA DA CIKKAKIYAR
BIYAYYA GA ALLAH. Allah yace:
Wanda yayi taqwa ga Allah. Shi
(Allah) zai sanya masa mafita
(Suratut-Thalaq)
3) HAKURI DA TABBATA KAN
GASKIYA. Don Annabi yace
wadannan kwanaki ne na hakuri
“Ayyaamus-Sabr”
4) ADALCI GA MASOYI DA
MAKIYI. Allah yace: Idan zakuyi
Magana kuyi adalci.
5) ADDUAH. Rokon Allah ginshiki
ne na warware matsala.
Yaa Allah ka kare Rayuwa, da
dukiya da mutuncin bayinKa
Salihai daga Munanan Fitintinu,

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

7 responses to “DABI'UN MUMINI A LOKACIN FITINTINU(Sheikh Isa Ali Pantami)”
 1. musabimam Avatar
  musabimam

  Malam allah yamaka sakaiya da gidan aljana,
  i-na da tambaya,
  shen dukkan musulmi muminine?

 2. Lawan Abdullahi Avatar
  Lawan Abdullahi

  Malam Allah yasaka da alkhairi amen.

 3. Abu ibrahim Avatar
  Abu ibrahim

  Mal jazakallahu khairan!

 4. Umar adam usman Avatar

  Assalama alaikum. Malam allha ya saka da alkhairi.

 5. Maharazu biniya Avatar
  Maharazu biniya

  Allah yasa kagama da duniya lafiya malam

 6. sadiq nuhu Avatar
  sadiq nuhu

  Malam Allah ya kara maka tsawon rai da aikata aiki nagari arayuwar ka yakareka daka sharrin duyiya da fitununta Yakuma sareka daga azaban kabari Allah yasa Aljannah firdausi itace makoma

Leave a Reply

Latest updates
Categories