KANA SON SASSAUCI DA SAUKI DA RANGWAME??(Sheikh Aliyu Said Gamawa)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

KANA SON SASSAUCI DA SAUKI
DA RANGWAME??
Allah mai girma da daukaka yana
kaddara sauki da sassauci ga
rayuwar bayin Allah nagari,Cikin
gudanar da dukkan harkokin
addinin su da rayuwar su. kuma zai
yi masu rangwame kan laifi da
kura-kuren su a gobe lahira.
Idan kana son yin rayuwa cikin
sauki, kuma ka samu rayuwa mai
dadi anan duniya da lahira to ka
dage wajen bin dokokin Allah cikin
dukkan al’amurran ka. Kuma ka
dogara ga Allah bisa dukkan
abinda ya same ka na qaddara mai
kyau ko maras kyau.
Kamar yadda kowa ke son samun
sauki daga matsalolin rayuwa, da
sassauci cikin komi, da rangwame
a wajen Allah haka ake son ka
lizimci wadannan dabi’u don
saukakawa waninka musamman
iyalai da makusanta. Pls muna
hakuri da juna, muna baiwa juna
uzuri, muna yafewa junan mu laifi
duk don neman yardar Allah.
Allah yana sauki ga masu yin
sauki, yana sassauci ga masu yin
sassauci, yana rangwame ga masu
yawan rangwame…. Allah ya bamu
iko, amin

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates