HAKURI IBADA NE(Sheikh Aliyu Said Gamawa)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

HAKURI IBADA NE:
Allah ya halicci dan adam akan
halaye dabam dabam, don haka
ake samun masu sauki da tsanani
cikin mu’amalar mu ta yau da
gobe.
Yana daga Cikin shiriyar Annabi
saw an nusar damu neman tsarin
Allah daga sharrin kawunan mu,
da miyagun aiyukan mu, don haka
duk wanda zakayi mu’amala dashi
to yana iya yi maka dai-dai, kuma
yana iya yi maka kuskure.
Mu sani duk wata tawaya, jinya, ko
laruri data same ka maganinta
shine ayi hakuri a mayar da abin
ga Allah.
Yana da wuya ace kullum sai anyi
maka yadda kakeso, ko sai kaji
abinda zaiyi maka dadi, ko sai idon
ka yaga abinda zai faranta maka
rai. Don haka rayuwa sai ka hada
da hakuri akan komi.
Hakika Ba wanda kuskure ko
matsala ba zata riskeshi ba cikin
harkokin rayuwar sa a tsakanin sa
da iyalan sa, ko makusantan sa, ko
al’ummar da yake raye a cikin ta.
maganin kowacce irin damuwa
shine hakuri, addu’a da mayar da
al’amarin ga Allah.
Gamuwa da kunci, wahala, tsanani
da damuwa duk mai yiwuwa ne ga
kowa gwargwadon yadda aka
qaddara masa, kuma ba wanda zai
iya kaucewa abinda aka qaddara
masa na sauki ko tsanani a
rayuwar sa, don haka anan ma
hakuri da duk halin da ake ciki
shine mafita ga kowa..
Mu sani hatta juriyar ibada, bin
umarnin Allah, koyi da Annabi saw,
biyayya ga iyaye, nisantar miyagun
aiyuka, kyautatawa iyalai da dangi
na kusa dana nesa, duk sai an
daure, anyi juriya da hakuri mai
yawa.
‘Yan uwa mu sani ba wanda zai
zamo mai hakuri face an bashi
lada mai yawa game da hakurin
sa, kuma an daukaka darajar sa,
mutumcin sa ya karu, ya hutar da
zuciyar sa, zama dashi zaiyi sauki
da dadi, dabi’un sa zasu zamo abin
sha’awa, kuma zai zamo abin
misali nagari, kuma abin koyi ga
kowa musamman zuriyar sa.
Hakuri yana gyara zaman iyali,
yana karfafa zumunta, yana
maganin fitina da tashin hankali,
yana kawo sulhu da yafe laifi, yana
gadar da halaye nagari, yana
inganta zaman makwabta, yana
haifar da alheri mai yawa duniya
da lahira.
Hakuri na lada shine wanda aka yi
shi don neman yardar Allah, da
wanda akayi shi ana cikin fushi ko
damuwa, da hakurin abinda kana
iya ramawa ko daukar fansa.
Lallai Allah yana tare da masu
hakuri, kuma anyi masu tanadi na
lada mai girma da aljannah a
wajen ubangijin su.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories