TAIMAKON JUNA IBADA NE, MUSAMMAN SHAYARWA(Sheikh Aliyu Said Gamawa)

·

·

TAIMAKON JUNA IBADA NE,
MUSAMMAN SHAYARWA:
Lallai yana daga cikin aiyuka
nagari da ladan su yana tabbata
ga mutum har bayan an mutu a
samar da ruwan sha ga mutane da
tsirrai da dabbobi da bishiyoyi.
Mu duba fa Allah yayi gafara ga
wata karuwa data shayar da kare
ruwa, pls to yaya wanda ya shayar
da dan adam ruwa?
Mu tuna shawarar da Annabi saw
ya baiwa wani sahabi cikin amsar
tambayar sa inda yake son yiwa
mahaifa sadaka bayan sun koma
ga Allah, Annabi saw yace ka
samar da ruwa ga al’umma sadaka
za’a akai ladan garesu ko da suna
lahira.
Hakika samar da ruwa ga masu
bukata nuna jin kai ne, kuma
kyautatawa ce, sannan nuna
tausayi ne, kuma tabbas kwadayin
lada ne, hakika zamu samu
sakamakon shayar da ruwa daga
Allah duniya da lahira.
Ina fatan hukumomi, mawadata,
‘yan kasuwa maza da mata,
ma’aikata, da sauran ‘yan uwa mu
himmatu koda ta hanyar da za’a
hada kai jama’a a tara kudin samar
da ruwa, yana da kyau mu dage
akan haka don alherin zai amfane
mu duniya da lahira.
Allah yasa mu ji, kuma mu aikata,
amin

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: