Jagoranci(Sheikh Aliyu Said Gamawa)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Rayuwar al’umma tilas tana
bukatar jagoranci, yadda za’a raya
al’ummar wajen kula da addini da
rayuwar kowa cikin aminci da dadi.
Don haka ake fatan samun jagorori
nagari ga kowacce al’umma, kuma
ya tabbata a nassi cewa Allah yana
baiwa kowacce al’umma jagorori
ne irin ta daga cikin su. Pls mu
duba yanzu a wani Hali kasar mu
ke ciki..? Kuma minene mafita..?
‘Yan uwa idan muna son samun
mafita da tsira to tilas ne mu koma
ga Allah wajen tsarkake shi da
Ibada, kuma hakanan cikin
gudanar da addinin mu mu nisanci
bidi’a da kirkirarrun al’amura, sai
gyaran halaye da kula da tarbiyya.
Kuma mu dage da addu’a Allah ya
gyara mana zukata da halayen mu
ya bamu shugabanni na kwarai.
Duk Wanda ke ganin wani laifi ko
kuskure to ya kawar gwargwadon
Hali da damar sa, ko da bakin sa,
ko yaki abin yayi ta fatan gyaruwar
sa. Surutai ba gyara ko fatan gyara
ba alheri bane garemu duka, kowa
ya dubi nasa matsalar ya tuna
gamuwar sa da Allah ya gyara.
Ikon Komi yana hannun Allah shi
kadai, kuma ba abinda yafi karfin
gyaruwar sa daga Allah.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

2 responses to “Jagoranci(Sheikh Aliyu Said Gamawa)”
  1. Halilu Hamidu Avatar

    assalamu alaikum warahamatullahi wabarkatuhu. yan uwa musulmi muhada kanmu a kalmar musulunci mu daina kungiyanci.

  2. SADIQ AHMAD ABUBAKAR Avatar
    SADIQ AHMAD ABUBAKAR

    Malam Allah ya biya

Leave a Reply

Categories
Latest updates