WAYE BAYA SON KANSA….?(Sheikh Aliyu Said Gamawa)

Danna nan domin shiga karatu Online

WAYE BAYA SON KANSA….?
Allah yayi dan adam da tulin
bukatu na rayuwa don gudanar da
rayuwar yau da gobe musamman
kayan jin dadi, da son samun sauki
da ‘yanci, da hutu, wassu har son
nishadi da walwala. Na tabbata ba
mai yiwa kansa fatan wahala, da
kunci, ko matsi da tsanani cikin
dukkan harkokin rayuwar sa.
Don haka kowa ke ta kokarin
samun dacewa wajen neman
alheri da albarka daga Allah cikin
gudanar da rayuwar sa da iyalan
sa.
Amma abinda muke mantawa
shine kowa abinda ya shuka anan
Duniya shi zai girba a lahira. Wato
in khairan ya aikata ya samu
khairan, in ma sharran ya aikata ya
samu sharran. Allah baya zaluntar
kowa. Duk wanda ya zabi jin dadin
duniya ta hanyar da Allah ya
haramta, to hakika ya zamo tamkar
wanda baya son kan sa. Don ya
zabi jin dadi kadan, da rayuwa mai
iyaka, ya jefa kansa cikin azaba da
wahala ta har abada.
‘Yan uwa mu hankalta, mu fadaka,
mu dinga duba aiyukan mu, mu
sani tabbas komi ana rubutawa,
kuma za’a tambaye mu aiyukan
gabobin mu, harshen mu, da
zukatan mu. Kada mu yi ta
kutsawa cikin sabawa Allah, kuma
mu dauka muna son kan mu!

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates