Kula Da sana'a(Aliyu Said Gamawa)

·

·

Domin neman ƙarin bayani danna nan

Yan uwa mu dage wajen kulawa
da sana’oin mu, don akwai lada
Mai yawa wajen Neman halal.
Hakika duk Wanda ya fita
kasuwanci, ko sana’ar sa ta
Neman abinci to zai samu
taimakon Allah da kuma albarka
cikin rahamar Allah garemu.
Sai dai babu alheri ga dukiyar da
aka sabawa Allah wajen tarata, da
sarrafata.
Yan uwa masu sana’oi kowa ya
natsu yaga da wacce irin dukiya
yake ciyar da Kansa da iyalan sa
da ita,, kuma da wacce irin dukiya
yake tufatar da kansa da sauran
dawainiyoyin rayuwar sa?
Yan kasuwa a nisanci algus, karya,
zamba, boye aibi da duk wata
hanyar da addini ya haramta
mana.
Hakanan maaikatan hukuma ku
rike amana, kuyi gaskiya, ku
nisanci rashawa, da cin dukiyar
gwamnati Akan karya, ana zuwa
aiki akan lokaci, babu uzuri ga
masu cin dukiyar haram daga
baitul malin hukuma wai don basu
da hanyar samun kudi sai ta
haram..!
Wallahi kowa za’a tambaye shi
dukkan abinda ya mallaka wato
yadda ya tara da yadda ya
sarrafata.
Ina mana tunatarwa kowa ya nemi
abin yi kada zaman banza ya
kaishi ga cin dukiyar mutane Akan
karya ko yaudara, ko wani dabo-
dabo, ko ta ha’inci.
Rahamar Allah ta wadaci kowa da
Komi, duk Wanda ya nema Allah
zai bashi, sannan ga albarka da
lada cikin dukiyar halal.
Pls kowa ya nemi abinyi don
zaman banza abin ki ne a
musulumci, kuma mutuwar zuciya
ne, da Dora nauyi Akan al’umma.
Maza da mata, Yara da Manya mu
sani kowa bayan ilimi na addini,
abinda keda matukar muhimmanci
shine Neman hanyar rayuwa Mai
tsabta daga dukiyar halal.

Leave a Reply

Latest updates
Categories