WAYE BAYA SON SAMUN RABO NA ALHERI..?(Sheikh Aliyu Said Gamawa)

·

·

WAYE BAYA SON SAMUN RABO
NA ALHERI..?
Allah ya dora mana yin azumi a
cikin dukkan watan Ramadan don
mu samu rabo mai yawa na lada
da kuma samun a kankare mana
zunubbai da ‘yantuwa daga wuta,
da sauran rabo na alheri mai yawa.
Hakika barin ci da sha a cikin
wunin watan Ramadan tsoron
Allah ne da komawa gareshi, kuma
aka kwadaidar da mu sallolin nafila
na tarawihi, da yawaita sadaka da
kyauta, da kokarin tilawar kur’ani,
ga halartan tarukan karatu. Lallai
cikin wannan akwai neman lada da
kusaci ga Allah mai yawa.
Hakanan aka umarce mu da
nisantar miyagun aiyuka, rufe
bakunan mu daga zagin wani ko
aibata wassu ko jin waqe waqe da
kade kade, da ashar ko amfanin da
harshe ko gabobi a sabawa Allah.
Kuma yana daga cikin rabo mai
yawa na lada da ake samu a watan
Ramadan wajen nunka kyautatawa
iyaye, iyalai, ‘yan uwa dangi,
makwabta da sauran al’ummar da
ke kusa da kai. Kuma ana son
kowa ya sanya dukiyar sa a
wannan wata cikin tallafawa
mabukata, marayu, marasa gata
da duk wani mai rauni mabukaci.
Shugabanni kuna da dama mai
yawa ta samun lada a wannan
wata mai albarka na kusanto sauki
da alheri ga alummar ku. Hakanan
malamai ku kwadaitar da al’umma
falalar sadaukar da kai wajen
taimakawa jama’a a wannan wata
mai albarka.
Duk matakin da kake ciki mazan
mu da matan mu pls mu himmatu
wajen isar da alheri ga junan mu,
ko da ta hanyar hada kai mu tara
wani abu na gudumawa mu ciyar,
mu tufatar da junan mu a wannan
wata. Mu yawaita abin buda baki a
masallatan mu, mu ciyar da masu
rauni da abin sahur da buda baki.
Shin wannan dama ta alheri mai
yawa na ibada, da kyautatawa pls
waye baya son ya samu!!!?

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: