BADA SADAKA SAI SALIHAI MASU RABO(Sheikh Aliyu Said Gamawa)

·

·

BADA SADAKA SAI SALIHAI
MASU RABO:
Allah yayi mana baiwa da mallakar
dukiya ne a matsayin falala da
rabo na alheri da aka kaddarawa
kowa iya nasa. Kuma rabo irin na
Allah wassu gasu da dukiya da
yawa wassun mu kadan, wassu
kuma ba Komi kullum sai an fita an
nemo ko da na kalacin kowanne
wuni, Sannan samun mallakar
dukiya Maiyawa ko ‘yar kadan ba
alama bace ta Imani ko samun
yardar Allah. Abin so ga rayuwar
musulmi ya tabbatar ya mallaki
Komi ta hanyar halal. Kuma mafi
sharrin dukiya itace wadda aka
sabawa Allah a hanyar tarata da
sarrafata.
Cikin alkur’ani, da hadisai anyi
mana umarni da Neman falalar
Allah ta dukiya, in an dace mun
samu kuma to mu sarrafata wajen
Neman yardar Allah da yin rayuwa
Mai tsabta mu da iyaye, iyalai da
sauran makusanta, kuma muyi
aiyukan Gina addini. Mu sani sai
Wanda Allah yaso shi da alheri ne
yake iya bada dukiyar sa wajen
aikin addini da Gina al’umma
musulma.
Hakika masu dukiya daga cikin mu
sun tafi da lada, tun da suna
kowacce irin Ibada kamar mu,
sannan suna karawa da sadaka,
mu kuma bamu da dukiyar bada
sadaka. A’a abin da ake so kowa
iya damar sa, da karfin sa ya
tabbata ya ciyar, ya yi sadaka ga
al’umma, kuma ya shigo aiyukan
Gina addini.
Lallai mu sani matsin hannu,
kankamo, rowa da boye dukiya
baa Ibada da ita, ko sadaka ko
aikin addini to wannan dukiyar ta
zama tabewa, halaka, da aikawa
Kai masifu da jarrabawa iri iri.
Kuma shine sanadin halaka da
wayewa a duniya da lahira. Allah
ka rabamu da makusanci Mai rowa
ga alumna da rowa ga aikin addini.
Mamakin Wanda ke rowa ga
Wanda ya bashi.
Siffa ta bayin Allah na kwarai
wajen mallaka da sarrafa dukiya
shine aiki da umarnin Allah,
nisantar sabawa Allah, da
kwadayin nema da samu Bisa
koyarwar addini. Allah baya Hana
Mai bayarwa, kuma yawan kyauta
da sadaka basa jawo talauci.
Hasali ma alheri da albarka ne ke
karuwa kan dukiyar Mai yawan
kyauta da sadaka. Kuma a tsare
masa dukiyar daga dukkan masifu.
Yan uwa muyi Komi da dukiyar mu
don Allah, mu sani dukkan aiyuka
suna tare da niyya. Kuma kowa
za’a saka masa ne gwargwadon
kyawun nufin sa, don ilimin Allah
ya kewaye Komi har cikin zukatan
mu. Duk Wanda ya aikata alheri
Komi karancinsa za’a saka masa
da wani alherin fiye da nasa.
Mu dage wajen yawan sadaka da
kyauta, don SALIHAN bayi da aka
tsarkake zukatan su ne ake samun
masu yawan alheri, da
kwadaitarwa dashi ga wanin sa a
cikin su.

One response to “BADA SADAKA SAI SALIHAI MASU RABO(Sheikh Aliyu Said Gamawa)”
  1. SADIQ AHMAD ABUBAKAR Avatar
    SADIQ AHMAD ABUBAKAR

    Malam Allah ya saka da Alheri

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: