ZAQIN IMANI(Sheikh Aliyu Said Gamawa)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

ZAQIN IMANI:
Allah Bisa ikon sa, da hikimar sa
ya zabi wassu daga bayin sa yayi
masu baiwa da dacewa da dan-
Dana zaqin Imani, wato suka samu
kansu musulmi, masu miqa wuya,
da cikakkiyar yarda da Allah, da
mayar da dukkan yadda zasuyi
addini da rayuwa suna yi ne kamar
yadda Allah ya umarta ta harshen
Annabi saw Bisa koyarwar
magabata na kwarai.
Mu sani kololuwar dandana zaqin
Imani shine, yarda da Allah
ubangiji abin bauta shi kadai,
kuma musulumci shine addinin ka,
sannan Annabi saw shine Annabi
saw abin kauna, da bi da koyi a
gareka.
Wanda ya dace da wannan baiwa
hakika ya rabauta, kuma ya dace
da tafarkin tsira. Abinda zai karawa
wannan daraja armashi shine
kokarin Neman ilimi Mai amfani da
aiki dashi.
Tir da Wanda aka masa wannan
gata don Allah yana son sa, amma
yayi rayuwar Kara zube na kin
sanin addinin Allah, kuma ya
shagala da aiyukan zunubi a
rayuwar sa.
Madallah da iyaye na kwarai, da
malamai na Allah masu shiryar da
al’umma, da hukumomi-shugab
anni masu damuwa da makomar
alummar su a gobe lahira.
Allah yasa mu dace, amin

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories