Soyayya Da Kiyayya Don Allah(Sheikh Aliyu Said Gamawa)

Danna nan domin shiga karatu Online

Yan uwa mu sani fa soyayya da
kiyayya suna da matukar girman
matsayi game da Imani, da addinin
mu.
Ana so da kin Komi, da Kowa ne
don Allah. Wato tun daga can cikin
zuciya da jiki ya zamo Neman
yardar Allah ne ya karkatar da Kai
zuwa ga so da kin Komi da kowa.
Mu sani hakika gobe lahira zamuyi
bayanin dukkan abinda muka so,
kuma da abinda muka ki a rayuwar
mu. Yana da kyau kullum muna
addu’ar Allah yasa muna soyayya
da kiyayya don Allah a junan mu,
da kuma duk abinda ya shafi
yadda muke gudanar da rayuwar
mu.
Mafi hatsarin so da ki shine Wanda
akayi don yaudara, karya, kwadayi,
ko sha’awar sabawa Allah da
bijirewa dokokin addini.
Muji tsoron Allah Maza da mata
mu yi soyayya da kiyayya Bisa
koyarwar addini, mu zamo masu
kyamar fadawa tarkon shaidan
wajen sanya son zuciya, da boye
gaskiya cikin so da ki a tsakanin
mu. Kowa fa duk abinda ya shuka
shi zai girba.
Ina mana bushara da cewa kowa
yana tare da Wanda yake so a
ranar lahira.
Kuma mu sani fa daga abinda kake
so da ki, da Wanda kake so da ki,
da dalilin ka na so ko kin ka ga
komi da kowa ake gane Kai
wanene.
Hakika da son juna don Allah, da
kin juna don Allah ake samun
shiga inuwar al’arshin Allah gobe
lahira.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates