SHIRIN BARIN DUNIYA:(Sheikh Aliyu Said Gamawa)

·

·

SHIRIN BARIN DUNIYA:
Allah ya kaddarawa duk mai rai
dandanan mutuwa, kuma aka
boyewa kowa rana, lokaci, gari da
sanadin mutuwar mu. Kullum muna
raguwa daidaya har a iso kaina,
kai ma a iso kan ka. Duk mai
tsoron mutuwa ko gudunta ya sani
Allah ya hukunta kowa tabbas sai
ta riskeshi.
Idan wani ya rigani sai in dunga
jimamin yadda yasa tufa da kansa
gashi ana tube masa don wanka,
in ga jikin nan da ake wanka da yi
masa ado an cusa shi a rami an
bisne, naga ‘yan uwa da masoya
sun juyo sun bar mutum a cikin
matsatstsen raminsa daga shi sai
halin sa da aiyukan sa.
Kwana kadan sai naga an fara
manta shi, masu kuka sun dawo
dariya, masu hawaye sun goge
suna cewa mi ya bari, yaya za’ayi
da gidan sa, bayan watanni matar
sa tayi adon neman wani mijin, ‘ya
‘yansa a fara kiran su marayu. In
macce ce mijinta a matsa masa ya
auro wata, zuriyar data bari su
dawo hannun wata, dukiyar ta a
raba, miji ya tare da amarya yana
ta murna..
‘Yan uwa mu sani kullum kara kusa
muke da komawa ga Allah. Kuma
tabbas anan duniya ake tanadin
samun sauki da dadin lahira.
Hakika da aiyukan mu na gabobi,
harshe da zuciya za’a yi mana
hisabi.
Muji tsoron Allah, mu dinga
inganta imanin mu ta hanyar
tsammanin kullum ba zamu kai
karshen wuni ba, in dare yayi
muna kaddarawa ba zamu kai
gobe ba. Ko in muna aiki mu dauka
shine na karshe..
Allah yasa muyi karshe mai kyau,
yasa mu dave duniya da lahira,
amin

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: