Tsarkake Bauta Don Allah(Sheikh Aliyu Said Gamawa)

Danna nan domin shiga karatu Online

‘Yan uwa mu sani an halicci mutum
da aljani ne don mu bautawa Allah
shi kadai. Kuma bautar tilas ta
kasance bisa umarni da koyarwar
Annabi (SAW). Farkon abin da
yake wajibi akan kowanne mutum
da aljani shine mu inganta imanin
mu, sannan mu san farillai na
wajibi da aka halicce mu domin su.
Dukkan hanyoyin samun lada, da
ibada na wajibi, da aiyukan da ke
samar da yardar Allah suna
karbuwa ne kawai in anyi su bisa
ilimi da ikhlasi. Mu ji tsoron Allah
ya bayin Allah muyi komi don
neman yardar Allah shi kadai.
Hasara ta tabbabta ga mai yawan
ibada don nuni ga mutane, ko mai
taimako da dukiya da ciyarwa ga
mabukata don ace yana da kirki,
da mai jarumta wajen yaqi ba don
Allah ba sai don ace shi jarumi ne,
ko mai aiyukan gina addini na
wa’azi da shiryarwa don ace shi
malami ne. Mu sani Allah shine
masanin fake da bayyane, yasan
abinda zukata suka boye, babu
abin da ke zuciyar wani ko cikin
furuci na hikima ko yaudara da zai
buya ga Allah.
In ko mun san haka ‘yan uwa yaya
muke aikin da zai zamo ba lada sai
wahala da fadawa halaka? Mi
mutumin da ka burgeshi zai iya yi
maka na sakamako gobe lahira?
Shin wadanda ka yaudara cikin
aiyukan ka da maganar ka anan
duniya yaya zaku kare gobe lahira
a gaban Allah? Mun manta RIYA
shirka ce karama? Yanzu kana
wahala don tara aikin da za’a
watsa shi kamar qura a ranar
lahira?
Mu kula da kan mu, mu ji tsoron
Allah, muyi ibada da gabobin mu
don neman yaradar Allah, muyi
kowanne furuci kan gaskiya da
tsarkin zuciya, mu tsarkake
zukatan mu yayin niyyoyin dukkan
aiyukan addini tasakanin mu da
Allah shi kadai. Allah mai rahma ne
mai jin kai, dukkan abinda bawa ya
tuba Allah zai iya yafe masa, kuma
lokacin tuba da gyara zuciya baya
wucewa har sai anzo gargara,
kowa yayi nadama kan laifin sa,
mu tuba gaba dayan mu, mu rayu
cikin kwadayi da tsoro har mu
koma ga Allah. Kada ka damu da
sai an yaba maka wannan ma wata
jinya ce mai tauye imani.
Hanyar kubuta daga fadawa RIYA
sune: Kada kana neman shahara
ko girma. Kada ka nemi fin kowa
da jin kafi karfin kowa, ka nisanci
girman kai, ka gujewa son duniya
ko kwadayin kayan mutane, ka
kauracewa son nishadi da holewa,
ka rabu da raina mutane, ka
kyamaci hassada da yawan gulma
ko yada zance da son kirkiran
karya.
Allah ya kara mana shiriya, yasa
karshen rayuwar mu yafi farkon
kyau a wajen Allah. Kullum muna
fata dauwama cikin shiriya, da
ROKON ALLAH YA KARBI
AIYUKAN MU NA IBADA, AMIN!
AMIN! AMIN

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

One response to “Tsarkake Bauta Don Allah(Sheikh Aliyu Said Gamawa)”
  1. Fararu sa'adu Avatar

    Allah yasaka da alheri.amiinn

Leave a Reply

Categories
Latest updates