WANE NE MALAMI NA ALLAH..?(Sheikh Aliyu Said Gamawa)

Danna nan domin shiga karatu Online

WANE NE MALAMI NA ALLAH..?
Malamai magada Annabawa, ba
su gaji komi ba sai ilimi, da kokarin
isar dashi ga al’umma ba don
neman yabo ko don kowa ya biya
su ba sai Allah.
Wani dan uwa yace mani, malamai
nada sa ido, kullum sai fadin laifin
mutane, ga su da saurin kore
mutum daga addini kamar nasu.
Nace haka kake fahimta ko? Yace
mani Eh…! Sai nace masa amma
yadda abin yake shine suna
kokarin tunawa mutane abinda aka
hana su ne don kada mutanen su
halaka. Kasan mai wa’azi ga
mutane kamar mai yin bayin ruwa
ne ga dashe, in mai bayi ya daina
zuba ruwa ga iccen zai bushe,
haka zuciya zata bushe in ba’a
tunatar da ita. Yace gaskiya haka
ne.
Sai yace to yaya ake gane malami
na Allah? Nace masa kasan
karkatacciyar bishiya bata bada
miqaqqiyar inuwa, wato malamin
da baya bin sunnar Annabi saw da
wuya a samu shiriya daga gareshi.
Daga nan naci gaba da ce masa:
Ku daina yawan zargin malamai,
ku sani fa shiriyar addini ta dora
mu akan tafarkin nagarta da
kokarin yin komi don neman yardar
Allah. Malami na kwarai da kake
tambayata akan sa zaka sameshi
da kokarin bin abinda ya sani na
addini, da yawan ibada, da son
kiran al’umma zuwa ga shiriya, da
nuna damuwar sa wajen hana
miyagun aiyuka.
Ka sani Ba’a gane malami na Allah
da shaharar sa, ko yawan
bayyanar sa ga jama’a. Illah mi
yake fadi kuma mi yake aikatawa?
malami na Allah zaka ganshi yana
da kokarin kiyaye harshen sa daga
karya, da maganar wani, ko
ha’intar al’umma cikin wa’azin sa.
Kuma dukkan magabata na kwarai
cikin malamai basu mayar da
wa’azi da malumtar su sana’a ba,
illa sun dauketa ibada ce da
neman yardar Allah.
Daga nan hirar mu ta kare, pls in
kaine yaya zaku yi da wannan
abokin hira tawa? Thnks

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates