SADAKA DA YAWAN KYAUTA BASA KARE DUKIYA(Sheikh Aliyu Said Gamawa)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

SADAKA DA YAWAN KYAUTA
BASA KARE DUKIYA:
Allah ya yi dan adam da son alheri,
da kuma kin kunci ko wahala,
sannan ga tsoron talauci ko shiga
wahala a rayuwa. Don haka ake ta
fafutuka na neman falalar Allah ta
dukiya don aji dadin gudanar da
rayuwa. Wato kowa yana kan tasa
hanyar nema na sana’a, ko
kwadago, ko dai duk wata hanya ta
juya dukiya ko jawota ta dama da
haggu.
Allah yana zaban wassu cikin
bayin sa ya arzutasu da rabon
dukiya mai yawa ta wani sanadi
cikin hanyoyin nema da muke kayi.
Wassu sun dace sun tara dukiya ta
halal, wassu kuwa sun tabe
dukiyar su ba tsarki wato ba halal a
ciki, wassu kuwa su hado naman
rago dana alade a tukunya guda
su dafa suna ci wato masu
gauraya halal da haram.
Tsabta irin ta addinin mu ta
munana dukiyar haram garamu, an
sanya ta kazantace abin kyama,
tana kai mai ita ga halaka da
gamuwa da fushin Allah. Madallah
da rayuwar magabata na kwarai
masu gudun dukiyar haram ga
kansu da iyalan su, saboda tsoron
dukiyar haram har gujewa abin
duniya sukeyi gaba daya don suyi
rayuwa mai nagarta da tsabta ta
neman yardar Allah da rahmar sa.
Duk wanda Allah ya bashi dukiya
ta halal ya godewa Allah ta hanyar
bayar da hakkin Allah a ciki,
sannan ya yawaita sadaka ga
marayu, mabukata da marasa
gata. Kuma ana kyautatawa
iayaye, iyali, dangi, makwabta, da
duk wanda yazo neman taimako.
Shaidan yana cusawa wassu masu
dukiya rowa, matsin hannu,
qanqamo da kin tallafawa kowa. To
mu sani hakika dukiya da duk
arzikin duniya na Allah ne, shiya
baiwa wanda yaso a cikin mu, don
haka mubi shiryarwar addinin mu
wajen yawan alheri, da kwadaitar
da junan mu yawan sadaka da
kyauta. Lallai sadaka da kyauta
basa kawowa mai dukiya komi
cikin dukiyar sa sai karin albarka,
da yawaita…!

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories