YAYA TSAKANIN KA DA AL'UMMA.?(Sheikh Aliyu Said Gamawa)

Danna nan domin shiga karatu Online

YAYA TSAKANIN KA DA
AL’UMMA.?
Rayuwa ta alheri Mai dadi da
albarka naga Mai kyautata alaqar
sa da kowa, ta hanyar baiwa kowa
hakkin sa. Madallah da Mai
budewa al’umma kofar alheri,
kuma mai toshe duk wata hanya ta
sharri da fitina ga kowa
gwargwadon koyarwar addini.
Ana son mutum Mai sauki da
sassauci cikin mu’amala, Mai
nagarta da yawan alheri na kyauta
da sadaka, mai yawan fara’a da
karba uzuri, Mai kamewa da
natsuwa.
Kuma mu sani ba’a son musulmi
ya zamo mai tsanani da saurin
ganin laifi, ko yin gaba da mutane,
yawan fushi, ko yawan gulma da
yada asirin mutane, wulakanci da
tozarta wani, korafi da kananan
magana, Rowa da daure fuska.
Ana so mu so juna, muna yiwa
juna wasicci da gaskiya, mu zamo
makusanta na kwarai da rayuwar
mu zatayi tasiri na alheri ga junan
mu, kada mu zamo masu barna ta
hanyar batar da juna, ko sauwake
aiyukan zunubi ga jama’a.
Ma’aunin da zaka gane amfanin ka
ga alumma shine duba yawan
gudumawar ka wajen samar da
alumma musulma, da aiyukan gina
addini. Kuma kana nazarin yaya
tsakanin ka da al’umma wajen
zaman yau da gobe?

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates