ZUWA GAISUWAR MARAR LAFIYA BABBAR IBADA NE(Sheikh Isa Ali Pantami)

·

·

Imam Bukhari, Shaykhul Islam da
Ibn Uthaymeen (Rahimahumul
Laah) dukkansu sun tabbatar da
cewa zuwa gai da majinyaci wajibi
ne. Amma Bn Uthaymeen (RH)
yana ganin cewa yana halatta wani
ya wakilci wani a gaisuwa ko kuma
zuwan wasu yasa wajibcin ya
sauka kan wasu “Fardhu
Kifaayah.”
Annabi (SAW) yana cewa: ku ciyar
da Mai Jin Yunwa, ku ziyarci
MARAR LAFIYA, sannan ku yanta
Fursunoninku (Bukhari).
FALALAR ZUWA GAISUWAN:
Annabi (SAW) yana cewa: Duk
wanda yaje gaisuwa ga marar
lafiya da SAFE, Mala’iku dubu
saba’in zasu masa Addu’ah har
zuwa yamma. Idan yaje da Yamma
Mala’iku dubu saba’in zasu masa
Addu’ah har gari ya Waye. Kuma
ana masa TANADIN LAMBU a
ALJANNAH. (Tirmithiy, Sahihun ne
a cikin Sahih Tirmithiy).
Annabi (SAW) ya kara da cewa:
Lalle Musulmi Idan ya ziyarci Marar
Lafiya to yana tafiya ne a cikin
inuwar Aljannah har sai ya dawo.
(Muslim).
Yaa Allah ka bamu ikon zuwa
gaisuwa ga marassa lafiya

5 responses to “ZUWA GAISUWAR MARAR LAFIYA BABBAR IBADA NE(Sheikh Isa Ali Pantami)”
 1. KHALIL YUSHA´U ABDULLAHI Avatar
  KHALIL YUSHA´U ABDULLAHI

  Its very very good 2 deliver GOD´s message nomatter how little its, may ALLAH bless us ALL.

 2. Marwan B. Kabir Avatar

  Ameen Ya Sheikh

 3. Abubakarlawan Avatar
  Abubakarlawan

  ALLAH YABAMU IKON ZUWA GIDA MARAR LAFIYA AMEEN

 4. Kabir ibrahim Avatar
  Kabir ibrahim

  [A decission can enfly by good right faith ] maa sha allah we kept thank god due to occuring of such sheikh like malam isah aliyu pantami

 5. […] Source: ZUWA GAISUWAR MARARLAFIYA BABBAR IBADA NE(Sheikh Isa Ali Pantami) […]

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: