Tafsirin Suratul A’ala Aya ta 16-17: Fifita rayuwar duniya akan lahira

Allah maɗaukakin sarki yace:

{ بَلۡ تُؤۡثِرُونَ ٱلۡحَیَوٰةَ ٱلدُّنۡیَا (16) وَٱلۡـَٔاخِرَةُ خَیۡرࣱ وَأَبۡقَىٰۤ (17) }

[Surah Al-A`lâ: 16-17]

Fassara/Sharhi

Yadda lamarin yake shine: Kuna fifita rayuwar duniya, Alhali Lahira shine mafi alheri kuma mafi wanzuwa

Wannan Ayah tana koyar damu cewa a koda yaushe mu rinƙa fifita rayuwar lahira akan duniya, domin ita rayuwar duniya ba komi bace idan aka kwatanta da lahira, domin ita ɗan wani jin daɗi ne kaɗan, kuma yini ɗaya daga cikin yinin lahira kamar Shekaru dubu ne idan Aka kwatanta ta na duniya. Kamar yadda Allah ya bada labari.

Lallai yini ɗaya a wurin ubangijinka kamar Shekaru dubune wanda kuke ƙidaya wa

Suratul Hajj: 47

Wannan yake nuna cewa wannan rayuwar duniyar ba komi bane, Jarabawa ce kawai Allah yake yi wa bayi. Shiyasa mai hankali baya ɗaukan duniya A matsayin wurin zama, yana rayuwa ne kamar baƙo yana shiri ko yaushe zai iya barinta. Kamar Yadda Annabi Sallallahu alaihi Wasallama ya faɗa wa Abdullahi Bin Umar :

Ka kasance a duniya kamar baƙo, ko matafiyi, Ibnu Umar ya kasance yana cewa idan ka wayi gari kada kayi tsammanin zakayi yammaci, idan kayi yammaci kada kayi tsammanin zaka wayi gari, kayi amfani da lafiyarka kafin rashin lafiya tazo maka, kayi amfani da rayuwar ka kafin mutuwa tazo maka.

Sahihul Bukhari: 6416

Sannan mu sani cewa duk wani abinda muka samu a duniya sai an tambaye mu akansu, Sabida haka kada mu ɗauka Kawai cin banza ne. Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yace:

Diga digan ɗan Adam bazasu gushe ba ranar tashin Alqiyama har sai an tambaye shi game da dukiyarsa, Ta yaya ya same ta, sannan ta yaya ya ciyar da ita

Sahihut-Tirmidhi: 2417

Duk dukiyar da mutum ya samu a duniya sai anyi masa tambayoyi akansa, ta yaya ya samu? ta halal ne ko ta harama? Sannan ta yaya yayi amfani da dukiyar? Ta Halal ko ta Haramun?

Sannan kuma Samun duniya bashi yake nuna cewa Allah yanason bawa ba, domin Allah yana bada duniya ga wanda yake so dama wanda baya so. Domin duniya ba komi bane a wurin Allah, bata kai fiffiken ƙuda ba.

Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yace: da ace duniya ta kai matsayin fiffiken ƙuda awurin Allah, da bai bawa kafiri kurɓan ruwa ɗaya ba

Sahihut-Tirmidhi:2320

Wannan yake nuna cewa Duniya ba komi bace, sabida haka don ka sami duniya bashi yake nuna kana da matsayi awurin Allah ba, domin manya manyan masu kuɗin duniya ba Musulmi bane, bal ma basu da alaƙa da Addini baki ɗaya duk da haka Allah ya basu dukiya fiye da kowa.

Abin Lura baki ɗaya shine Tsoron Allah. Wanda yafi girma awurin Allah shine wanda yafi tsoron Allah.

A koda yaushe ya zamo lahira ce a gaban mu ba duniya ba.

Wannan kuma bashi yake nuna cewa zamuyi watsi da duniyar baki ɗaya ba, A’a zamuyi amfani da duniyar ne gwargwadon buƙata, sannan kuma muyi amfani da ita domin samun lahira, duk abinda zamuyi a duniya ya zamto muna yi ne domin Allah, da zuciya mai kyau da ikhlasi.

Addinin Musulunci yana buƙatar masu kuɗi, masu ilimi a fannoni daban daban, Sabida haka lokacin da Allah ya buɗa maka wani hanya sai kayi amfani da wannan Hanyar domin neman lahirarka, bawai kawai domin tara duniya ba, domin baka san yaushe ne mutuwa zata zo maka ba. Allah yasa mudace.

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: