Ta yaya zamu gane gaskiyar Al-Qur-ani?

Mai rubutu: Hamza Diso


Dalilan da suke nuni akan gaskiyar ƙur’ani suna da yawan gaske, wanda ta taƙaitaccen rubutu bazai bada dama a faɗi adadi mai yawa daga cikinsu ba, amma dai ga wasu daga ciki.

  1. sanannen abu ne cewar an haifi shugaban mu Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) a Makka, wanda a wancan lokaci matattara ce ta jahilci da bautar gumaka, waɗanda suka iya karatu da rubutu a garin gaba ɗaya an sansu saboda ƙarancin su, to a guri irin wannan Annabi ya taso kuma bai rabu dasu yayi tafiya ba kafin Annabci sai sau biyu kawai, ɗaya yana yaro ƙarami, karo na biyu kuma yana saurayi kuma kasuwanci ne ya fitar dashi sannan kwanaki kaɗan yayi ya dawo, ƙara akan haka cewar Annabi baya karatu baya rubutu, kenan bazai iya karanta littattafan magabatansa ba kuma bashi da malami balle yaji wani ilimi daga gareshi, gashi kuma waɗanda yake rayuwa dasu manyan jahilai ne. Idan ka fahimci wannan to ta ina kake ganin zai iya samo littafin daya ƙunshi nau’ika daban-daban na ilimi? Ilimin rabon gado kaɗai zaka iya gama jami’a amma shi baka gane shi ba!! Kana ganin wanda yayi rayuwa irin wacce na faɗa maka a sama zai iya ƙirƙiro shi?
  2. Alƙur’ani ya ƙunshi abubuwan da ɗan Adam bai iya gano su ba sai da aka samu ci gaba na ilimi, misalin haka: matakan halittar yaro a cikin mahaifiyarsa da kuma bayani akan yadda ƙarƙashin Teku yake alhali Annabi bai taɓa zuwa bakin Teku ba, wa kake ganin ya gaya masa abinda yake ƙarƙashin sa??
  3. bada labari akan abinda zai faru gaba kafin ya faru, misali: Buɗe garin Makka, cin nasarar yaƙin da Rumawa zasu yi a ƙasa da shekara goma masu zuwa, kuma hakan ya faru kamar yadda ya faɗa, yiwa musulmi bushara cewa zasu mallaki ƙasashe masu yawa a lokacinda su ɗin basu da aminci akan kansu, amma sai gashi abin ya faru kamar yadda ya faɗa, dama wasu labaran dayawa bayan waɗannan
  4. tahaddi da ƙur’ani yayi na cewa idan kuna ganin ba daga Allah yake ba to ai kuma mutane ne irin Annabi, idan kun isa ku ƙirƙiro irinsa amma suka kasa, kuma har yanzu ƙofa a bude take ga duk wanda yake ganin zai iya
  5. Alƙur’ani ya sauka acikin shekaru 23 amma babu banbanci tsakanin farkon sa da ƙarshen sa, wanda da ace Mutun ne ya rubuta to da Yakamata a samu banbanci don dole a waɗannan shekarun mutum ya samu ci gaba kuma usulubinsa ya sauya
  6. yawan ayoyin ƙur’ani da kuma daɗewa da yayi yana sauka amma kuma babu kuskure ko ɗaya a cikinsa, kuma har yau ƙofa a bude take idan akwai wanda yake ganin akwai kuskure sai ya faɗa
  7. Alƙur’ani ya ƙunshi Abubuwan da babu su acikin littattafan magabata wanda haka yake nuna ba a cikinsu aka kwafo ba, misali bayani akan Shugabannin mu guda biyu Annabi Hudu da kuma Annabi Saleh
  8. Alƙur’ani yayi bayani dalla-dalla akan abubuwan da suka faru na tarihi a wasu ƙasashen da Annabi bai taɓa zuwan su ba
  9. Alƙur’ani ya dinga yiwa Addinai na baya gyara akan guraren da sukayi kuskure kuma ya bayyana abubuwan da malaman su suka ɓoye, kana ganin wanda baya karatu baya rubutu zai iya wannan??
  10. Alƙur’ani ne kaɗai littafin Addinin dayake lura da ɗabi’ar ɗan Adam, ta yadda bai manta da duniyar mutum ba sannan baiyi watsi da buƙatar rai ba ( wato yana lura da gangar jiki da ruhi baki ɗaya).

Kadafa ka manta da cewar wanda yazo dashi ba a taɓa tuhumar shi da ƙarya ko cin Amana ko ha’inci ba.

Don neman ƙarin dalilan akan gaskiyar ƙur’ani da kuma ɓacin kiristanci karanta wannan littafin:


(Yanzu baza suyi tuntuntini akan ƙar’ani ba? Da ace daga wanin Allah yake da kaga saɓani dayawa a cikinsa.) Annisa’i: 82

Allah ya tashe mu muna masu imani da Alƙur’ani

Click Here to Support our work

Leave a Reply

%d bloggers like this: