Sako Zuwa ga Wani mai Kore samuwar Allah

By: Hanmza Diso

Barka da yamma Mr ________, Ina fatan ka yini cikin koshin lafiya.

Da farko Ina tayaka murnar kasancewar ka cikin masu bibiyar inda gaskiya take, Ina fatan zaka zamo mai bin tsagwaron dalili, kuma inayi maka albishir cewar mu (musulmi) kasuwar mu tafi ci idan za ayi aiki da ilimi da kuma lafiyayyan hankali.

Abu na biyu: kayi kuskure guda biyu

1. kuskure na farko kayi zaton cewar dole idan akwai Allah to lallai sai ya amsa bukatarka kuma yayi maka yadda kake so.

2. kuskure na biyu shine kayi gini akan kuskuren farko kace tunda bai amsa maka ba to Babu shi. Idan Mr_______ yasan wani abu cikin Aristotelian logic ( term logic) a Babin syllogism to zaka San cewar duk abinda mutum ya Sanya cikin Premises to shi zai girba a conclusion, kuma koma a common sense ai bazai Yiwu mutum ya shuka dawa ya girbi Alkama ba!! Idan har ka karanta wani Abu cikin iliman hankali to lallai kasan wannan, idan Kuma baka Sani ba to da wani hankalin ka gano abinda kake kai?

Ko dai wani ne ya gano maka?

Kuskuren farko kayi shine ta fuska biyu

1. ka hada tsakanin samuwa da kuma aiki, wanda wadannan abubuwa ne masu banbancin gaske, ba sharadin samuwa bane shi samammen yayi wani abu.

2 kayi zaton cewar dole ne akan Allah- idan har akwai shi – to dole ne ya shiryi bayinsa!! Shi kuma Allah babu wani abu dayake dole akansa, Don idan har akace ga wani abu dole yayi to ya tashi daga Allah Kenan, don Ai ma’anar kasancewar sa Allah itace shine Kawai zai sa ayi abinda yaga dama kuma yadda yaga dama.

Wata kila Ina fadar wannan maganar zaka iya

Yin caraf kace yawwa kaga ai bashi da Rahama Kenan! don da yana da rahama ai da yayi abinda zai zamo maslahar bayinsa!! Ni kuma sai nace maka ka sake Yin wani kuskuren daka hada tsakanin rahama da irada da hikmah. Allah yayi halitta da manufa da kuma hikmah, ya wajabtawa bayinsa su bauta masa don su samu sakamako mai kyau, to amma tun da jarrabasu yayi nufin yi sai ya nuna musu hanyar dai-dai ta wahayi ya kuma nuna musu kuskure, ya kuma halicci shaidan mai batarwa sannan ya halicci mala’iku masu kokarin kinsawa mutum aikin Alkhairi, ya halicci dalili na shiriya ya kuma halicci shubuha ta batarwa, sai ya bawa bayi hankali Wanda zasu iya banbance zare da abawa, idan ya dora kowa akan shiriya to menene amfanin jarabawar? Sannan tunda akace maka jarabawa to lallai kasan cewar akwai masu ci akwai masu faduwa, Ina zaton wannan ma ai common sense zai iya riskar haka Ka huta lafiya.

Click Here to Support our work

Leave a Reply

%d bloggers like this: