Sukar Bukhari da Muslim

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Mai rubutu: Hamza Diso


Naji wani mutum cikin kokarinsa na sukar bukhari da Kuma yada shi’ancin sa yana cewa:

“Bukharin da kuke cewa tsarkakke ne ya Ruwaito hadisin Isma’il bn abi uwais

An ruwaito hadisin nasa ne Don ya ruwaito abinda yake da alaka da khilafa wato hadisin ” ku umarci Abubakar yayiwa mutane sallah

shi Isma’il makaryaci ne..”

Abu na farko daya kamata kowa ya sani shine; mazajen isnadin bukhari da Muslim sun kasu Kashi biyu

  1. wadanda ake kafa hujja dasu, wadannan sune riwayar su take a matsayin Usul
  2. wadanda ake ruwaito maganar su don karfafar ruwayoyin Kashi na farko, wannan yasa imamul Bukhari ya ruwaito hadisin mutane irinsu Ahmad bn yazid bn Ibrahim da ubayyu bn Abbas bn sahl da Asid bn Zaid da sauransu, su wadannan ba dogaro akeyi da riwayarsu ba, a’a karfafarta ake da wasu ruwayoyin.

Duk Wanda yake da alaka da ilimin hadisi yasan wannan, idan mutum ya koma tarjamar Muslim ko ya koma muqaddimar Alminhaj zaiga amsar da imamu Muslim ya bayar sanda aka ce masa menene dalilin dayasa ya ambaci mutane masu rauni acikin littafinsa.

Wannan yasa ake banbancewa tsakanin masu ruwayar ba duka ake cewa Siqat bane, Amma hadisan Bukhari dukkan su ake cewa sun inganta, Kuma duk mutanan mu sun san cewar raunin isnadi baya nuna raunin matani don akwai yiwuwar samun wani isnadin daban

Bayani akan wannan mas’ala yana da tsaho Amma duk dalibin hadisi yasan wannan!

Abu na biyu: Isma’il bn Abdillahi malamin Bukhari ne, kuma dukkanin hadisan da Bukhari ya ruwaito daga gareshi acikin mutaba’a ne ba acikin Usul ba sai hadisai guda biyu kacal, Suma Kuma sun inganta saboda dalilai dayawa, ba nan ne gurin ambaton su ba, Amma daga cikin dalilan akwai kasancewar shi Isma’il da kansa ya bawa Bukhari usul dinsa Don ya fayyace masa dai-dai da kuskure.

Abu na uku: Hadisin Umartar Sayyidina Abubakar (Allah ya Kara masa yarda ya kunyata makiyansa) da ya jagoranci sallah yazo ta hanyoyi daban-daban ba wai ta hanyar Isma’il kadai ba, kenan ruwayar da kake surutu akanta an fitar da itane fitarwar mutaba’a da shawahid.

Abu na Hudu: Malaman jarhu wat-ta’adil sunyi sabani akan Isma’il ba wai an hadu akan raunanashi bane kamar yadda kake son ka nunawa gama garin da suke maka ihu, Kuma karya da ake magana-idan ta tabbata- ai yayi tane lokacin kuruciya Kuma ya tuba.

Idan kana son raunana hadisi ya kamata ka koyi yadda tsarin ilimin yake, ci da karfi da kakeyi babu inda zai Kai ka

Allah ya shirya mabiyanka mutanan kirki da muka sani wadanda rashin fahimta yasa suke biye maka

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories