ME YA FARU A KARBALA 357(Dr. Mansur Sokoto)

Danna nan domin shiga karatu Online

Mu Koma Kan Yazid
Nuni ya gabata a can baya zuwa
ga irin sabanin mawallafa a game
da Yazid. Bisa ga wannan ne
mutane suka kasu kashi uku a kan
shi. Wasu na zagi har ma da
la’antar sa, wasu na yabon sa da
gwarzanta shi. Kashi na uku su ne
wadanda suka tsaya a tsakani
suna neman ayi masa adalci a
ajiye shi a matsayin sauran ire-
irensa daga cikin sarakunan
musulunci masu rauni wadanda
suka tafka kurakurai a cikin
mulkinsu. A sa su a cikin ayar da
madaukakin sarki yake cewa
( ﻭﺁﺧﺮﻭﻥ ﺍﻋﺘﺮﻓﻮﺍ ﺑﺬﻧﻮﺑﻬﻢ ﺧﻠﻄﻮﺍ ﻋﻤﻼ ﺻﺎﻟﺤﺎ
ﻭﺁﺧﺮ ﺳﻴﺌﺎ ﻋﺴﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻥ ﻳﺘﻮﺏ ﻋﻠﻴﻬﻢ ﺍﻥ ﺍﻟﻠﻪ
ﻏﻔﻮﺭ ﺭﺣﻴﻢ( ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻟﺘﻮﺑﺔ: ١٠٢
“Kuma wadansu sun yi ikirari da
laifukansu, sun gauraya aiki na
kwarai da wani maras kyawo, yana
yiwuwa Allah ya yi tuba a kan su,
lalle Allah Mai yawan gafara ne,
mai gamammen jinkai”. Suratut
Taubah: 102
Mu saurari wani daga cikin
malamai masu irin wannan
matsakaicin ra’ayi, shi ne Imam
Abu Abdillahi Adh Dhahabi. Ga
abinda ya ce a cikin tarihin Yazid a
littafinsa SIYAR A’LAM AN
NUBALA (7/36):
ﻟﻪ ﻋﻠﻰ ﻫﻨﺎﺗﻪ ﺣﺴﻨﺔ ﻭﻫﻲ ﻏﺰﻭ ﺍﻟﻘﺴﻄﻨﻄﻴﻨﻴﺔ،
ﻭﻛﺎﻥ ﺍﻣﻴﺮ ﺫﻟﻚ ﺍﻟﺠﻴﺶ، ﻭﻓﻴﻬﻢ ﻣﺜﻞ ﺍﺑﻲ ﺍﻳﻮﺏ
ﺍﻻﻧﺼﺎﺭﻱ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ… ﺍﻟﻰ ﺍﻥ ﻗﺎﻝ: ﻭﻳﺰﻳﺪ
ﻣﻤﻦ ﻻ ﻧﺴﺒﻪ ﻭﻻ ﻧﺤﺒﻪ، ﻭﻟﻪ ﻧﻈﺮﺍﺀ ﻣﻦ ﺧﻠﻔﺎﺀ
ﺍﻟﺪﻭﻟﺘﻴﻦ، ﻭﻛﺬﻟﻚ ﻓﻲ ﻣﻠﻮﻙ ﺍﻟﻨﻮﺍﺣﻲ، ﺑﻞ ﻓﻴﻬﻢ ﻣﻦ
ﻫﻮ ﺷﺮ ﻣﻨﻪ ..
Tare da tubatubansa yana da
alheri guda daya, shine yakin
Qustantiniyah. Kuma shi ya
jagoranci yakin, alhali a cikin
rundunar akwai manya irin su Abu
Ayyub Al Ansari (mai masaukin
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa
Alihi Wasallam).. Har dai inda
Dhahabi ya kai ga cewa, “Yazidu
na cikin wadanda ba ma zagin su,
ba ma kuma kaunar su. An yi ire-
irensa da dama daga cikin halifofin
daulolin guda biyu (yana nufin
Umawiyyawa da Abbasiyyawa).
Haka ma a cikin gwamnoni an yi
ire-irensa da ma wadanda shi ya
dara su dama.
A baya mun kawo hadisin da ya
nuna falalar wannan jihadi da su
Yazidu suka yi wanda Bukhari ya
ruwaito shi – hadisi na 2924 – daga
Ummu Haram Al Ansariyyah matar
sayyidina Ubada bin Samit wadda
ta ce, Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wa Alihi Wasallam ya ce
“Runduna ta farko daga al’ummata
wadanda zasu yi yaki a kan teku
an gafarta masu. Sai na ce, ya
Manzon Allah, ni ina cikinsu? Ya
ce, eh, kina cikinsu. Sannan ya ce,
kuma runduna ta farko daga
al’ummata da zasu yaki birnin
Qaisar – Qustantiniyah – su ma an
gafarta masu. Na ce, Manzon Allah
ina cikinsu? Sai ya ce, a’a. Kuma
mun fadi ba ta ga wannan yakin da
Yazidu ya jagoranta ba don ta cika
bayan gama wancan yaki wanda
babansa Mu’awiyah ya jagoranta
kai tsaye. Kamar yadda bakin da
ba ya karya ya fada mata.
La’antar Yazid
Game da la’antar Yazid kuwa da
ma la’antar kowane irin musulmi –
kai har da kafiri – ba aikin mutanen
kirki ba ne. Domin kuwa
manzonmu Sallallahu Alaihi Wa
Alihi Wasallam ya ce a hadisin
Abdullahi bin Mas’ud Radiyallahu
Anhu: “Musulmi ba mai yawan
suka ne ba, ba mai yawan la’anta
ne ba, ba kuma mai fadin kazamar
magana ne ko kalmar alfasha ba”.
Imam Al Bukhari ya ruwaito shi a
cikin AL ADABUL MUFRAD, Hadisi
na 312, haka ma Ibnu Hibban a
cikin Sahihin littafinsa (1/421)
Hadisi na 192, haka ma Imam
Ahmad a cikin MUSNAD (1/404)
da kuma Tirmidhi a cikin SUNAN
(4/350), Hadisi na 1977. Albani da
Arna’ut sun inganta shi.
Magabata da dama sun kasance
suna kame bakinsu daga la’antar
ko da dabba ce, domin watarana a
cikin tafiye tafiyen Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wa Alihi
Wasallam ya ji wata mata ta la’anci
rakumarta don ta kusa kayar da ita,
sai ya yi umurni a dauke kayan da
ke kan rakumar a sake ta. Ya ce,
“An riga an la’ance ta”. Imran bin
Husain da ya ruwaito Hadisin ya
ce, yanzu haka kamar ina ganin ta
tana tafiyarta kowa ya fita batunta.
Duba SAHIH MUSLIM (8/23),
Hadisi na 6769.
Wannan game da la’antar wani
wanda aka ayyana kenan. Amma a
Jumlace ana iya cewa, Allah ya
la’ani azzalumai, ko Allah ya la’ani
makaryaci, ko mai cin rashawa ko
makamancin haka. Amma a kama
sunan wani a la’ane shi, wannan
shine ake kyama. Domin la’anta na
nufin nisantar rahamar Allah.
Rahamar Allah kuwa da ita ce zai
iya samun tuba in har yana raye,
da ita ne kuma zai samu sassafci
idan ya riga mu gidan gaskiya.
Wani muhimmin al’amari da ya
kamata mu yi nuni gare shi a nan
shi ne tasirin farfagandar JAISHUT
TAWWABIN da muka ambata a
baya na karin gishiri ga mafi yawan
labaran abubuwan da suka faru.
Misali, masu tantance ruwayoyi
sun yi suka ainun ga riwayoyin da
suka ce, an je da kan sayyidina
Husaini har birnin Sham wurin
Yazid, ballantana sauran almarar
da aka hikaito ta cewa ya fashe
haushi, da nuna murna har da
wasu baitoci na rashin kunya.
Haka kuma game da iyalan
Husaini bai inganta cewa, an yi
masu wulakanci ba ko dan kadan.
Maimakon haka ma da aka zo da
su wurin Yazidu ya mutunta su,
kuma ya yi masu rantsuwa cewa
bai yi umurni da haka ba, bai kuma
ji dadi ba.
Dangane da waki’ar Harra wadda
a cikin ta Yazid ya halalta Madina.
A nan ma rundunar Tawwabuna ta
yi karin gishiri matuka ga
abubuwan da suka faru har da
cewa, an yi ma mata fyade abinda
sam ba abu ne da aka sani a
wannan lokacin a cikin al’ummar
musulmi ba. Haka ma kan
rundunar da ta je Makka ba abinda
ba a fada ba a kan ta. Sawa’un
rundunar da muka yi magana a
kan ta ta Ibnu Numair ko wadda
Hajjaju ya jagoranta daga baya.
Har cewa aka yi sun rusa Ka’aba
alhalin masana sun dade da
wargaza wadannan karairayi. Kun
dai ji cewa ita wannan runduna ko
shiga Makka ba ta yi ba suka samu
labarin Allah ya halaka Yazid. To,
ta ina za su rusa Ka’aba?!

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates