ME YA FARU A KARBALA 11(Dr. Mansur Sokoto)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Me ya sa aka nada Yazid?
Muka ce sanin gaibu sai Allah.
A iya dan nazarin da Allah ya bada
iko ban yi tuntube da wata riwaya
da shi sayyidina Mu’awiya ya
bayyana dalilinsa na yin haka ba.
Mutane kuma sun kasu kashi biyu
dangane da wannan sabon abu da
sakataren manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wa Alihi Wasallam ya yi.
Masu kyautata masa zato suka ce,
mai yiwuwa dayan wadannan
abubuwa ko dukansu na cikin
dalilansa:
1. Mai yiwuwa ya ji tsoron afkuwar
fitina a tsakanin musulmi bayan
cikawar sa la’akari da sabon
yanayin da al’umma take ciki,
musamman bayan an fadada
biranen musulunci, mutane da
dama sun shigo wadanda ba su da
kyakkyawar manufa ga ci gaba da
daukakar addini. Maimakon ya bari
ayi ka-ce-na-ce sai ya ayyana
dansa bisa ijtihadinsa.
2. Kwarewar da YAZIDU ya nuna a
sha’anin shugabanci da rikon
jama’a. Musamman da yake ya yi
Amirul Hajji shekara goma kafin
haka, ya kuma jagoranci mafi
girman rundunar da ta kwace
hedikwatar babbar super power ta
duniyar wancan lokaci. Husaini
yana cikin sojojin Yazid kamar
yadda muka fadi. Ba wannan yakin
kawai aka yi da Husaini a zamanin
Mu’awiyah da sauran halifofi ba.
Sauran yakokan ma kamar yakin
Tabaristan da Fustat da Tarabulus
duk ya halarce su a matsayin soja.
Kai, tun a lokacin halifancin
sayyidina Usman shi da wansa Al-
Hasan sun halarci yakin Ifriqiyah a
karkashin jagorancin Abdullahi bn
Sa’ad bn Abi Sarh. Duba: Tarikh
Dimashk na Ibn Asakir (14/111) da
Al-Wafi Bil Wafiyyat na Safadi
(12/262) da Al-Bidaya Wan Nihaya
na Ibn Kathir (8/161) da kuma
Tarihin Ibn Khuldun (2/128). A cikin
littafan Shi’a kuma sai a duba:
Hayatul Imam Al-Husain (A.S) na
Baqir Sharif (1/394) da Al-Akhlaq
Al-Husainiyyah na Ja’afar Al-
Bayati, shafi na 131.
3. Kasancewar Yazidu shi ne
wanda zai fi samun goyon bayan
mutanen Sham, cibiyar halifanci ta
wancan lokaci saboda matsayin
mahaifinsa wanda yake da
gagarumin goyon baya a can tun
da ya yi gwamna tsawon shekaru
ashirin, har kuma yanzu da ya hau
kujerar sarkin musulmi wasu
tsawon shekaru goma sha biyar
kafin ya ayyana dan nasa a
matsayin Yarima.
Ta bangaren masu ganin laifinsa
kuwa sun zarge shi ne da nuna
son kai, da sha’awar ya mayar da
mulkin musulunci gado, abinda duk
magabatansa ba su yi kokarin yi
ba. Shi ma sayyidina Ali da aka
nada dansa a bayansa ai ba shi ya
ce ayi haka ba. Shawara ce ta
gudana a tsakanin jama’arsa
bayan wafatinsa har suka cimma
wannan matsaya. Amma a ra’ayin
‘yan Shi’a da suka ce shine ya yi
ma sa wasici kenan shine ya fara
mayar da mulki ya zama gado.
A nan yana da kyau muyi nuni da
cewa, littafan Shi’a ma sun
tabbatar da cewa, bisa shawara
aka nada Al-Hasan ba bisa wasici
ba. Misali,Mahmudi a littafinsa
Nahjus Sa’ada (2/733) da kuma
Mas’udi a cikin Muruj Ad-dhahab
(2/425) duk sun kawo cewa, an ce
ma sayyidina Ali (A.S) zamu nada
Al-Hasan a bayanka, sai ya ce, ba
zan sa ku ba ba kuma zan hana ku
ba. To, ina maganar wasici?!
To, ko ya lamarin yake dai,
mutanen Sham sun bada hadin kai
sosai wajen aiwatar da wannan
muradi na Mu’awiyah. Haka ma
gwamnoni da kwamandojin da
suke jagorancin jihadi duk sai da
Mu’awiyah ya shawarce su suka
amince suka kuma mika hannunsu
suka yi mubaya’a ba tare da wata
jayayya ba. Al-Hafidh Abdul Ganiy
Al-Maqdisi cewa ya yi an samu
sahabbai 60 da suka amince da
nadin Yazid, suka kuma yi ma sa
mubaya’a.
Su kuma mutane hudu da basu yi
mubaya’a ba, an kyale su hakanan
ba wata takura ko tsangwama da
aka yi musu.
Wannan duka ya faru ne
Mu’awiyah Radiyallahu Anhu yana
da ransa da lafiyarsa a shekara ta
55H. Bayan da Allah ya yi masa
rasuwa kuma dukkan masu fada a
ji sun jaddada mubaya’a kai tsaye
ga Yazidu in banda biyu daga cikin
wadancan mutum hudu da muka
ambata. Shi dai Abdurrahman dan
sayyidina Abubakar Allah ya yi
masa cikawa kafin haka. Shi kuma
sayyidina Abdullahi dan Umar ya
hakura ya yi mubaya’a tare da su
Ibnu Abbas da sauran mutane. Ya
ce, daman ni ban yarda ayi sarki
biyu ne ba, amma yanzu tunda
mahaifinsa ya mutu, kuma al’umma
ta taru ta amince da abinda aka yi
to, ni ba ni da jayayya. Wadanda
suka rage kenan su ne HUSAINI
da Ibnuz Zubair, Allah ya yarda da
su.
Duba wadannan bayanan a cikin:
Tarikh Al-Islam, na Dhahabi
(3/147-152) da Tarikh Khalifa bn
Khayyat, tahqiqin Prof. Akram Al-
Umari, shafi na 213.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories