ALKAKI DA RUWAN ZUMA(Dr. Mansur Sokoto)

·

·

Ingantaccen Tarihin Sayyadi
Rasulullahi Sallallahu Alaihi Wa Ala
Alihi Wasallam
Bismillahir Rahmanir Rahim
Gabatarwa
Muhimmancin Wannan Tarihi
Tarihin manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wa Alihi Wasallam ya banbanta da
sauran tarihohi irin na manyan mutane
da jagorori da ake karantawa.
1. Da farko dai karanta wannan tarihi
ibada ne.
2. Madubi ne na rayuwar da Allah
Tabaraka Wa Ta’ala yake son mu
kwaikwayi irin ta.
3. Babu wata hanyar da take tabbatar
mana da gaskiyar wannan taliki da aka
aiko mana kamar karanta tarihin
rayuwarsa.
4. Babu kuma wata hanya da za ta
dawwamar da so da kaunarmu a gare
shi sama da nazarin rayuwarsa mai
albarka wadda take cike da ababen
girma da wani dan adam bai da irin su.
5. Sanin wannan tarihi mai albarka na
taimaka mana wajen sanin makamar
ayoyi da yawa da hadisai a cikin tarihin
fiyayyen halitta ta hanyar sanin dalilin
saukar aya ko munasabar da ta sa
manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa
Alihi Wasallam ya fadi hadisi, wanda
zai taimaka matuka wajen gane
hakikanin ma’anar nassi.
6. A cikin wannan tarihi ne zamu ga
irin gudunmawar da sahabban manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi
Wasallam suka ba shi da taimakonsa
da suka yi wajen isar da sakon
musulunci. Allah Tabaraka Wa Ta’ala
da kansa ya fadi cewa, da su ne ya
karfafe shi har ya samu nasarar
kafuwar addini (Suratul Anfal: 62 da
Suratut Taybah: 88).
7. Kamar yadda a cikin sa ne zamu ga
irin tarbiyyar da manzon Allah ya yi
masu bisa ga umurnin da maxaukakin
sarki ya ba shi a Suratu Ali Imran: 164
da Suratul Jum’ah: 2.
Kaicon mutanen da suka yanke
alakarsu da wadannan bayin Allah
wadanda manzon Allah ya tarbiyyantar
da su domin mu koyi tarbiyyarsa daga
wurin su. Mutanen da tarbiyyar
manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa
Alihi Wasallam ta kama jininsu da
tsokarsu har ta kai suka sayi aljannar
Allah da ayyukansu. Kamar yadda
Allah ya ce:
(( ﺇﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﺷﺘﺮﻯ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﺆﻣﻨﻴﻦ ﺃﻧﻔﺴﻬﻢ
ﻭﺃﻣﻮﺍﻟﻬﻢ..))
(Suratut Taubah: 111)
(( ﻟﻜﻦ ﺍﻟﺮﺳﻮﻝ ﻭﺍﻟﺬﻳﻦ ﺁﻣﻨﻮﺍ..))
(Suratut Taubah: 88-89)
Kuma Allah ya shelanta ya yarda da su
(Suratut Taubah: 100, Suratul Ma’ida:
6, Suratul Fathi: 18 da kuma Suratul
Mujadila: 22)
Su ne kuma Allah ya ba da shedar
abinda ke cikin zukatansu na gaskiya
da imani (Suratul Anfal: 63, Suratul
Fathi: 18-19).
Kuma Allah ya bayyana matsayinsu ya
banbanta da na sauran musulmi duka
wadanda ba su ba (Suratul Hujurat: 7).
Wai shin akwai wata daraja da kai ta
su bayan Allah Tabaraka Wa Ta’ala ya
ce ya lizimta masu “Kalimatut
Taqwa” (Ita ce kalmar shahada) ya ce
kuma sun fi kowa cancantar ta da zama
ma’abotanta?! (Suratul Fathi: 26).
8. Babu shakka sanin tarihin
gwagwarmaya da fadi-tashin kafa
addinin musulunci da aka yi tun
zamanin farko yana haskaka mana
tafarkin da ya kamata mu bi wajen
tsayar da addinin Allah. Da yawa a yau
akwai masu tunanin hanyar gyara ita
ce, mu kafa gwamnatin musulunci
sannan sai mu sa – da karfi –
gwamnatin ta gyara mutane. Sai mu ce
ma su a koma ga tafarkin Sirah, mu ga
yadda shugaban tafiya (SAWW) ya yi.
Haka lamarin yake ga abubuwa da
dama da suka shafi siyasarmu ta
da’awa da malanta da makamantansu.
9. Kamar yadda masu kira zuwa ga
musulunci ke samun miqaqqen tafarki
a cikin wannan tarihi haka su ma masu
tafiyar da mulki da jagororin al’umma
da masu fatauci da yan qwadago da
qungiyoyin sa kai.. Da maza da mata
da manya da qanana.. Kai, da ma kowa
da kowa.
10. Duk wata matsala da zaka shiga a
rayuwarka idan ka karanta tarihin
manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa
Alihi Wasallam za ka tarar da wata mai
kama da ita da hanya mafi sauqi ta
warware ta. Misali, maraici, talauci,
arziki, mulki, matsalolin aure, na
tarbiyyar ‘ya’ya, qalubalen siyasa da
fuskantar ‘yan adawa dss.
Haqiqa, duk musulmin da bai san
tarihin manzonsa ba zuwan sa a duniya
ya zama kamar zuwan zomo a kasuwa.

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: