ME YA FARU A KARBALA 18(Dr. Mansur Sokoto)

·

·

Husaini (R.A) A Hanyar Kufa
A kan hanyarsa ta zuwa Iraqi
sayyidina Husaini ya gamu da
shahararren mawakin nan
Firazdaq, ya tambaye shi inda ya
fito sai ya ce Kufa. Da ya tambaye
shi halin da ya baro a can sai
Firazdaq ya ce masa, “Zukatan
mutane na tare da kai, makamai na
ga masu mulki, sanin abinda zai
faru kuwa gaibu ne sai Allah”.
Da ya karasa gaba sai kuma ya
hadu da Hurru bn Yazid at-Tamimi
wanda ya fito fili ya ba shi
shawarar ya koma Makka. Har
sayyidina Husain ya karkata ga
wannan ra’ayi sai kuma hukuncin
Allah ya rinjaya, Husaini ya ci gaba
da tafiyarsa.
A wani wuri kuma da ya yada
zango sai ya hadu da Abdullahi bn
Muti’ shi ma yana dawowa daga
Kufa. Dan Muti’u bai yi wata wata
ba ya shawarci Husaini da
komawa Makka yana ce ma sa “Ka
ji tsoron Allah ya kai Husaini, ka
tsare martabar gidan manzon Allah
(S) kada ka keta ta. Kada ka je
Kufa, kada ka gitta ma mulkin
wadannan mutane. Idan ka yi haka
wallahi zasu iya kashe ka. Allah ne
kuwa kadai ya san karshen
wannan lamari idan ya faru”. At-
Tarikh al-Islami na Mahmud Shakir
(3/124).
Daga nan zamu fahimci cewa, ‘yan
Shi’ar Kufa ne suka nemi sayyadi
Husaini da ya je wajensu bisa
alkawarin zasu taimake shi su kare
shi a yayin da ilahirin mabiyan
Sunnah na wancan lokaci suka
roke shi kada ya amsa ma su. To,
idan har wannan tafiya ta haifar da
salwantar rayuwarsa da ta iyalansa
gami da sakacin wadancan da
suka gayyace shi, kai ma da sa
hannunsu, don Allah wa ke da
alhakin kisan su?

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: