ME YA FARU A KARBALA 16(Dr. Mansur Sokoto)

·

·

Kamar yadda muka gani a baya
mutanen Iraqi sun riga sun dauki
alkawari kakkarfa a kan cewa in
sayyidina Husaini ya zo wurin su
za su taimake shi kuma za su
halifantar da shi a madadin Yazid.
Sun aike masa wasiku masu dinbin
yawa a kan haka. Duk da zuwan
Muslim bn Aqil a garinsu ba a gane
mugun nufinsu ba. Abinda ya kara
sa sayyadi Husaini ya shirya tsaf
don tasar ma hanyar Kufa.
Masu nazari sun lura da akwai
hatsari a cikin wannan mataki da
jikan manzon Allah (SAWW)ya
dauka. Don haka Jabir dan
Abdullah da Abu Sa’id al-Khudri da
Abu Waqid al-Laithi da Umar bn
Abdirrahman bn al-Harith da
sahabbai da dama da suke Makka
a lokacin suka roke shi da kada ya
tafi. Akwai kuma wadanda suka
aiko masa wasiku daga wasu
garuruwa suna rarrashin sa a kan
haka kamar Abdullahi bn Jafar bn
Abi Talib da Amr bn Sa’id bn al-Ass
da wata mashahuriyar malamar
hadisi ta wancan lokaci ana ce ma
ta Amrah bint Abdirrahman.
Anya kuwa wadannan shawarwari
da nasihu sun yi amfani? Babu
shakka Husaini ya saurari
wadannan shawarwari da zuciya
wankakka sai dai kuma Kaddara ta
riga fata!

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: