ME YA FARU A KARBALA 22(Dr. Mansur Sokoto)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

A safiyar 10 ga watan Muharram
na wannan shekara da muke
magana a kan ta; shekara ta 62H
aka ja daga tsakanin rundunoni
guda biyu; rundunar sayyadi
Husaini (R.A) mai mutane kimanin
50 mafi yawansu mata ne da yara,
da kuma rundunar gwamnan Kufa
Ubaidullahi dan Ziyad mai kimanin
mayaka 4000.
Babban muradin rundunar Kufa a
wannan rana ita ce su kama jikan
manzon Allah (SAWW) a hannu
domin su kai shi – a daure – wurin
gwamnan Kufa. Amma da abin ya
ci tura sai Shamru ya bada koren
haske aka fara karawa. Sayyidina
Husaini (R.A) da jama’arsa sun yi
yaki na azo-a-gani domin kuwa
akalla sojoji 88 sun kwanta dama
daga cikin wannan tsinanniyar
runduna ta mutanen Kufa kafin
marece. Da farko mayaka suna ta
kauce ma sayyadi Husaini, amma
ganin irin hasarar sojoji da suka yi
kuma ba wata alamar saranda
daga wurin Husainin sai Zur’atu At
Tamimi wanda shi ma dan Shi’ah
ne ya kai ma Husaini sara a
kafadarsa. Sinanu dan Anas – wani
dan Shi’ar shi ma – ya zaburo ya
kai ma Husaini hari ga
makogaronsa. Sannan ya sare shi
a kirji. Kafin Husaini ya kai kasa sai
wani shaidani ana ce masa Khuli
Al Asbahi – dan Shi’ah – ya sa
takobi ya cire kansa. Allahu Akbar!
Shahadar sayyadi Husaini ta
tabbata ta hannun wadannan
azzalumai masu neman yardar
gwamnati ta hanyar saba ma Allah
mahalicci. Kada Allah ya yarda da
su baki daya.
Zamu kawo sharhin malaman
Shi’ah kan wannan lamari daga
littafansu, sannan mu je birnin
Sham don mu ji yadda Yazidu ya
tarbi wannan mugun labari.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

2 responses to “ME YA FARU A KARBALA 22(Dr. Mansur Sokoto)”
  1. me ya faru a karbala

  2. Bashiru A. Sanusi Avatar
    Bashiru A. Sanusi

    Assalamu alaikum mallam Dr. Mansur sokoto muna maka fatan alkhairi da kokarin da kakeyi wajen yada addinin musulunci Allah yasaka maka da alkhairi Allah yasa aljannan fiddausi shine mako marka amin, mallam don Allah kataimaka mana da tarihin me yafaru akarbalaha complete daga farko har karshe, a email dina.

Leave a Reply

Latest updates
Categories