ME YA FARU A KARBALA 3(Dr. Mansur Sokoto)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Wane ne YAZIDU?
Sunansa YAZIDU Dan Mu’awiyah
Dan Sakhr (Abu Sufyan) Dan Harb
Dan Umayyah Al Umawy Al
Qurashie. Ana yi masa alkunya da
Baban Khalid.
Mahaifiyarsa ita ce Maisun ‘yar
Bahdal daga kabilar Kalbu, daya
daga cikin kabilun Kuraishawa
masu karfi a wancan lokaci. Ta
rabu da mahaifinsa tana dauke da
cikinsa, sai ta yi mafarkin wata ya
fito daga jikinta. Masu Fassara
suka ce mata in har mafarkinki ya
tabbata za ki haifi sarki. Hakan
kuwa aka yi.
An haifi YAZIDU a shekara ta 26H
a zamanin halifancin sayyidina
Usmanu Dan Affan. YAZIDU ya
tashi a gidan sarauta, domin ko da
aka haife shi mahaifinsa yana
gwamnan Sham. Ya samu
tarbiyyar jihadi domin tun yana
matashi dan shekaru 24 ya
jagoranci runduna mafi girma da ta
fatattaki Rumawa kuma ta kwace
hedikwatarsu “Qustantiniyah”.
Daga nan ne kuma sunan YAZIDU
ya fara fitowa har ya yi tashe a
tsakanin matasa. A nan ne kuma
ya samu tasa daraja daga Hadisin
Ummu Haram bint Malhan Matar
sayyidina Ubada bin As Samit
wacce ta ce ta ji Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wa Alihi
Wasallam na cewa “Rundunar
farko da zasu yi yaki a teku daga
cikin al’ummata Allah ya gafarta
masu”. Ta ce, Manzon Allah ina
cikin su? Ya ce, eh. Kina cikinsu.
Sannan ya ce “Rundunar farko da
zasu ci birnin Qaisar daga cikin
al’ummata su ma Allah ya gafarta
masu”. Ta ce, Manzon Allah ina
cikin su? Ya ce, a’a. (Sahihul
Bukhari, Hadisi na 2924).
Wannan Hadisi ya hada falalar
YAZIDU da babansa gaba daya.
Domin kuwa babansa Mu’awiyah
ne ya fara jagorantar Rundunar
farko da ta yi jihadi da Rumawa a
teku, zamanin sarki Usmanu a
shekara ta 27H. A cikin rundunarsa
kuwa har da irin su Miqdadu Dan
Amru da Shaddadu Dan Ausu da
Abu Dharril Gifari da Ubada Dan
Samit tare da wannan matar da ta
gamu da ajalinta kai tsaye bayan
gama yakin.
Shi kuma YAZIDU shi ne ya ci
babban birnin Qustantiniyah a
shekara ta 52H. Qustantiniyah
kuwa ita ce birnin Qaisar a
zamanin Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wa Alihi Wasallam. A cikin
sojojin wannan runduna tasa kuwa
har da wasu fitattun sahabbai irin
su Ibnu Umar da Ibnuz Zubair da
Ibnu Abbas da Abu Ayyub al Al
Ansari, mai masaukin Manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi
Wasallam, Wanda kuma ya cika
kafin kammala yakin.
(Duba Fathul Bari na Al Hafizh
Ibnu Hajar 6/120 da kuma Al
Bidayah Wan Nihaya na Ibnu
Kathir 6/249).
Kafin haka YAZIDU ya yi Amirul
Hajji na musulmi baki daya a
shekara ta 50H.
Ba zamu yi mamaki ba idan muka
ga mahaifinsa ya zabe shi a
matsayin Yarima. To, amma ko
mene ne ya sa aka zabe shi alhalin
akwai wadanda suka fi shi daraja
irin su HUSAINI jikan Manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi
Wasallam da su Ibnu Umar da
makamantansu?
Wannan ita ce tambayar da zamu
amsa a nan gaba Sa’annan mu
dawo ma rikicin mawallafa da takin
sakar su a kan wannan dan taliki
YAZIDU kafin mu fantsama a cikin
maganar rikicin da ya hada shi
HUSAININ da YAZIDU wanda a
sanadiyyarsa Allah ya ba HUSAINI
shahada.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates