ME YA FARU A KARBALA? 4(Dr. Mansur Sokoto)

Danna nan domin shiga group na karatu Online

Rikicin mawallafa a game da
YAZIDU
Yana da wahala kwarai ka samu
mutum a tarihi wanda aka yi ta
takin saka a kansa, ruwayoyi kuma
suka rinka cin karo da juna a kan
sa kamar YAZIDU. Yawan
masoyansa masu yabon sa, da
makiyansa masu sukar sa na
sanya mai karatun tarihi a cikin
rudani ba na wasa ba. Zan bada
wasu ‘yan misalai don mu gane
wannan.
Misali na Daya: A yayin da Ibnu
Abdi Rabbihi ya ruwaito cewa,
YAZIDU ya damu da nadin da aka
yi masa a matsayin kwamanda
wajen yakin Qustantiniyah kuma
har ya zargi babansa da son
halaka shi. Kai har ma wai zambo
ya yi ma baban nasa! (Duba Al
Iqdul Farid na Ibnu Abdi Rabbihi
4/367)
Shi kuma Ibnu Tolon cewa ya yi
YAZIDUn ne ya nemi a ba shi
wannan mukami. Saurari
ruwayarsa kamar haka:
Watarana Fakhitah matar
Mu’awiyah ta zagi YAZIDU a
gabansa sai ya ce mata, ai
YAZIDU ya fi danki Abdullahi. Da
ta gardamta ma sa sai ya aika aka
kira Abdullahi a gaban ta don ya
nuna mata banbancin su. Da
Abdullahi ya zo sai ya tambaye shi
in yana da wata bukata. Abdullahi
sai ya kada baki ya ce, baba jaki
nake so ka saya min! Mu’awiyah ya
ce, to, kin ga irinta! Ai kai ma jaki
ne. Tashi ka ba ni wuri. Nan take
ya aika aka kira masu YAZIDU, sai
ya yi masa irin tayin da ya yi ma
dan uwansa. YAZIDU sai ya fadi ya
yi sujada don godiya ga Allah. Da
ya daga kansa sai ya taya babansa
murna da Allah ya nuna masa
wannan rana da ya amince ma
dansa na cikinsa. Sannan ya ce
masa, bukatocin dan sarkin
musulmi su ne kamar haka:
1. Ka shugabantar da ni a wajen
Jihadi
2. Idan kwarewata ta bayyana sai
ka yi mini Amirul hajji
3. Ka fada ma jama’a na nemi ayi
masu karin albashi kuma ka aminta
4. Ka yanka ma marayu sabon
tsarin albashi bisa ga rokona.
5. Daga baya sai ka ayyana ni a
matsayin yariman da zai gaje ka
(Duba littafin Qaidus Sharid Min
Akhbari Yazid na Ibnu Tolon, shafi
na 25-26).
Duda irin banbancin da ke tsakanin
wadannan ruwayoyi guda biyu. A
ta farkon an nuna YAZIDU a
matsayin wani wawa da bai san
ciwon kansa ba, har zambo yake
ma mahaifinsa saboda ya tura shi
yaki. A ta biyun kuma sai ya fito
wani sadauki, jarumi, mai tarin
basira da hankali, ga nazari da iya
siyasa. To, wace riwaya zamu
dauka?
Zamu ci gaba da kawo misalai irin
wadannan don mu tabbatar da
yadda marubuta suka sha banban
wajen bayyana wannan dan taliki
sannan daga bisani mu fadi
ra’ayinmu a kan sa. Bayan haka
sai mu koma maganar siyasa, ina
nufin nadinsa da Abubuwan da
suka haifu bayan sa.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Latest updates
Categories