ME YA FARU A KARBALA 33(Dr. Mansur Sokoto)

Danna nan domin shiga karatu Online

Matsayin Malaman Madina Game
Da Tawaye A Kan Sarki Yazid
1. Ibnu Umar:
Kamar yadda muka gani a baya
sayyidina Abdullahi dan Umar na
cikin wadanda ba su yi na’am da
nadin Yazidu ba. Amma da ya ga
jama’a sun yi masa mubaya’a a
bayan mutuwar babansa sai ya
kyamaci ya fita daban daga
al’umma. To, a lokacin da wannan
maganar ta taso ta yin tawaye kan
Yazid, Ibnu Umar sai ya tara
dukkan iyalansa ya yi masu
kashedi da sa hannu a ciki. Ya ce
kuma duk wanda ya shiga cikin
wannan fitinar zamu raba gari da
shi. Dalili kuwa shine mun riga
mun mika hannayenmu mun yi
masa mubaya’a bisa amincin Allah.
Ya ce kuma na ji manzon Allah (S)
yana cewa, “duk wanda ya yi
yaudara za a kafa ma sa tuta a
ranar alkiyama a ce ga yaudarar
da wane ya yi”. In ban da shirka
kuwa babu yaudarar da ta kai
kwance mubaya’ar shugaban
al’umma. In ji shi. Duba Sahihu
Muslim tare da sharhin Imam An-
Nawawi (2/1478) hadisi na 1851.
Sayyidina Ibnu Umar bai tsaya
kawai ga gargadin iyalansa ba.
A’a, sai da ya yi tattaki har wurin
jagoran yan tawayen; Abdullahi bn
Muti’u. Abdullahi ya yi wuf ya
dauko masa majingini, sai ya ce
masa dakata. Ni ban zo don in
zauna ba. Na zo ne in sanar da kai
wani hadisi da na ji shi daga
manzon Allah (SAWW) cewa, “duk
wanda ya zare hannunsa daga
biyayya (ga shugaba) zai gamu da
Allah ba shi da hujja. Kuma duk
wanda ya mutu yana mai rabuwa
da jama’ar musulmi to, zai yi
mutuwa irin ta jahiliyya. Sahihu
Muslim, hadisi na 1851

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates