ME YA FARU A KARBALA 28(Dr. Mansur Sokoto)

Danna nan domin shiga karatu Online

A Makka tun da labarin Karbala ya
je ma su sai Abdullahi bin Zubair
ya nemi goyon bayan jama’a a kan
zama khalifa. Kuma ya samu nan
take. Kamar dai mutanen Makka
na ganin duk gwamnatin da ta iya
tafka wannan danyen aiki to,
tawaye a kan ta ya zama wajibi.
A Madina birnin Manzo kuwa,
jama’a sun tashi haikan don nuna
alhininsu game da abinda ya faru.
Ba da bata lokaci ba suka tsige
gwamnansu Usman bin
Muhammad bin Abi Sufyan, suka
tattara duk dangin Banu Umayya
da ke zaune a Madina suka rufe su
a cikin gidan Marwan bin Al Hakam
zuwa wani dan lokaci kafin daga
bisani su kore su daga birnin
Madina baki daya. Wannan sai ya
zama matsayin wata matashiya ce
da kuma gargadi na soma tawaye
a kan gwamnatin Yazidu. Kuma an
ruwaito cewa adadinsu na da
yawan gaske.
Bayan sama da watanni goma da
aka yi ana famar sasanta wannan
lamari, mutanen Madina sai kara
cijewa a kan matsayinsu suke yi. A
nan ne Yazid ya tashi wata
runduna da ya yi mata izinin yakar
gari mai alfarma bayan gargadi na
kwana uku da ya amince a ba su
na su dawo ma doka. Wanda ya
jagoranci wannan runduna shine
Muslim bin Uqbah. A nan ne fa
Yazid ya iyar da kife sauran kimar
da yake da ita a idon jama’ar
musulmi na duniya a wancan
lokaci. Domin kuwa duk kokarin da
rundunar Muslim ta yi na shawo
kan mutanen Madina su koma ga
da’a ya ci tura. Masu shiga tsakani
duk suka hakura. Daga karshe
kaddarar Allah ta gudana da ayi
ta’addancin halasta wannan birni
da Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam ya haramta. An yi
hasarar rayuka da dama na
mutanen kirki masu ibada da
matasa da malamai har da wasu
daga cikin ‘ya’yan sahabbai. Bayan
da Muslim ya tarwatsa rundunar
mutanen Madina, ya karya karfin
mayakansu sai ya nada masu
sabon gwamna shine Ruhu bin
Zinba’u. Wannan kuwa ya faru ne a
farkon watan Dhul Hajji na shekara
ta 53H.
Da Muslim ya gama wannan barna
sai ya tasar ma birnin Makka mai
alfarma bisa ga umurnin sarki
Yazid domin tunkarar matsalar
Ibnuz Zubair. To, amma Allah bai yi
masa jinkiri ba tunda rai ya yi
halinsa tun yana kan hanya.
Wanda ya karasa tafiya da
rundunar shi ne Husaini bin
Numair. Sun isa Makka daidai
lokacin aikin hajji, suka je Minna
da Arafat, suka yi hadaya tare da
jifar Shedan. Amma fa ba hanyar
shiga Makka balle ayi dawafi da
sa’ayi tunda rundunar Ibnuz Zubair
ta yi zobe ta cikin garin Makka.
Haka su kuma Ibnuz Zubair da
jama’arsa sun yi dawafi da sa’ayi
amma ba zancen tsayin Arafat
tunda ba su iya fita wajen gari. Sai
aka yi canzaras; ba wanda hajjinsa
ya inganta a wannan shekarar. La
haula wala kuwwata Illa billah.
Watanni hudu rundunar Yazid na
fake da Makka, bayin Allah na ciki
suna shan azabar rayuwa, ba a
shiga ba a fita, sai ga ikon ubangiji
ya bayyana, labari ya iso cewa
sarki Yazidu ya gama da duniya.
Allahu akbar. To, ko ya wannan
kunyatattar runduna ta karasa da
Ibnuz Zubair da mutanen Makka?
Ku dakace mu.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates