ME YA FARU A KARBALA 37(Dr. Mansur Sokoto)

·

·

Hindu A Ranar Uhud
Kasancewar mun kira sunan
wannan baiwar Allah a cikin
zancen ta’addancin da aka yi wa
sayyadi Hamza kuma don tabbatar
da adalcin da muka yi alkawali tun
da farko a cikin wannan rubutu zai
dace mu yi nuni da cewa, game da
kisan sayyidus shuhada’i; Hamza
ya tabbata cewa an yi masa
“muthla” an farka cikinsa da shi da
sauran shahidai muhajirai guda
biyar da suka samu shahada a tare
da shi. Abinda Quraishawa ba su
wa Ansaru; mutanen Madina su 64
da suka samu shahada ba saboda
sun fi jin haushin wadancan
dangin nasu. Amma fa bai tabbata
cewa, Hindu ko maigidanta Abu
Sufyan suna da hannu a ciki ba.
Duk abinda ake fada na cewa,
Hindu – ita da matayen da ke tare
da ita – sun rika cire kunnuwa da
hancin gawawwaki har ta yi
warewari da ‘yan kunne da su a
maimakon nata da ta bai wa
Wahshi tukuicin kisan sayyadi
Hamza da ya yi, kuma da cewa ta
cire hantar sayyidina Hamza ta
tauna har ta kasa hadiyewa
sannan ta zubar.. Duk wannan bai
inganta ba domin asalin labarin
daga wurin Saleh bin Kaisan ne –
Malamin ‘ya’yan sarki a zamanin
Umar bn Abdil Aziz. Daga wurinsa
ne Ibnu Ishaq ya jiyo wannan
labarin ya rubuta a cikin littafinsa
na Sirah, daga nan kuma labarin
ya yadu. Shi kuma Ibnu Kaisan
sam bai riski faruwar wannan
lamari ba domin a lokacin ma ba a
haife shi ba, kuma ba a san daga
inda ya samu labarin ba. Riwayar
Imamu Ahmad ita ma a kan
wannan labari mai lahani ce kamar
yadda shaihin malami Ibnu Kathir
ya bayyana. Ka duba: As-Sirah An-
Nabawiyyah na Ibnu Hisham tare
da sharhinsa Ar-Raud Al-Unuf na
Suhaili, tahqiqin Abdur Raman Al-
Wakil (6/15) da kuma Musnad na
Imam Ahmad (6/191) da Al-Bidaya
Wan Nihaya na Ibnu Kathir (4/41).
Shi kuma Abu Sufyan (R.A) bayan
da aka kare yakin na Uhud ya gaya
ma musulmi cewa, zaku ga an
wulakanta gawawwakinku. Ku sani
ba ni na sa ayi ba, kuma ban ji
ciwon da aka yi ba. Wannan fa
kafin musuluntar sa kenan kamar
yadda muka sani. Sahihul Bukhari,
littafin yakoka, babin yakin Uhud
(7/350 Fathil Bari).
Wadannan dalilai suka sa Sheikh
Muhammad bin Abdallah Al-
Uwaishin ya kawo wannan labarin
a cikin littafinsa na kissoshin karya
a cikin Sirah, shafi na 147-152.
Abin da ya wajaba mu sani shi ne
wadannan bayin Allah duk sun
musulunta tare da sauran
Quraishawa a lokacin da aka ci
galaba a kan Makka kuma manzon
Allah (S) ya karbi musuluncinsu ya
yafe ma su duk cin zarafin da suka
yi ma sa shi da jama’arsa a baya.
Ya yi haka ne kuma bisa ga
umurnin Allah (Suratun Nahl:
126-128). Da wannan ya kasance
laifinsu an kankare shi gami da
shirka uwar laifuffuka.
Ku dakaci darasi na karshe; Me Ya
Dace Mu Yi A Ranar Ashura?

Leave a Reply

Latest updates
Categories
%d bloggers like this: